Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Ɗalibin Jami'a bisa Zargin Yiwa Iran Leken Asiri a Isra'ila

Asiri Ya Tonu: An Kama Wani Ɗalibin Jami'a bisa Zargin Yiwa Iran Leken Asiri a Isra'ila

  • Hukumomin tsaro a Isra'ila sun kama wani matashin ɗalibi da ke karatu a Jami'ar Ben Gurion bisa zargin yi wa Iran leƙen asiri
  • Ɗalibin wanda bai wuce shekara 22 a duniya ba, ya ce ya aikata hakan ne saboda tausayin falasɗinawa da Isra'ila ke kashewa a Gaza
  • A wata sanarwa da hukumar leƙen asiri da ƴan sanda suka fitar, sun ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Israel - Jami'an tsaro sun kama wani ɗalibi a Isra’ila bisa zargin yana yi wa kasar Iran leƙen asiri tun lokacin da ƙasashen suka yi musayar wuta a tsakaninsu.

Rahoton hadin gwiwa da hukumar leken asirin cikin gida ta Isra’ila, Shin Bet, da ‘yan sanda suka fitar a ranar Alhamis, ya tabbatar da kama ɗalibin.

Kara karanta wannan

Iran, China da Rasha sun yi taro yayin da Trump suka hadu a Netherlands

An kama ɗalibi da laifin leken asiri a Isra'ila.
Hukumomi sun cafke ɗalibin jami'a kan laifin yi wa Iran leken asiri a Isra'ila Hoto: Carin M. Smilk
Source: Facebook

Vanguard ta kawo rahoton cewa matashin mai shekara 22 na fuskantar tuhumar aikata laifukan da suka shafi tsaro tare da gudanar da wasu ayyuka a madadin wakilan Iran.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin ɗalibi da leƙen asiri a Isra'ila

Matashin, wanda ke karatun kwas ɗin, 'Information systems' a jami’ar Ben Gurion da ke Beersheba, ya fito ne daga ƙauyen Deir al-Asad, ƙauyen Larabawa da ke Arewacin Isra’ila.

An cafke shi tun watan a watan Yuni kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sai dai har kawo babu tabbacin cewa ko an kama shi ne kafin ko yayin rikicin kwana 12 da ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Iran a watan Yuni.

Idan ba ku manta ba, Iran da Isra'ila sun shafe kwanaki 12 suna musayar wuta tsakaninsu, lamarin da ya ja hankalin duniya.

Sai dai bayan Amurka ta shiga tsakani, an samu nasarar shawo kan ɓangarorin biyu har suka yarda suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Gaza: An gano yadda mutane 870 suka mutu a kwanaki 12 na yaƙin Iran da Isra'ila

Laifuffukan da ake zargin ɗalibin ya aikata

Hukumomin Isra'ila sun ce dalibin ya yi mu’amala da wani jami'in Iran na tsawon watanni.

Sun bayyana cewa bayan an ba shi wasu kuɗaɗe, ana zargin ya aikata wasu ayyuka na laifi da suka shafi tsaro karkashin umarnin wakilin ƙasar Iran.

Cikin abin da ake zarginsa da shi har da kokarin cutar da wani mutum, watsar da ƙusoshi a kan babban titi a Beersheba da kuma yaɗa maganganun da ka iya raba kan al’umma.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu.
Hukumomin Isra'ila sun shirya gurfanar da wani ɗalibi a kotu kan zargin yiwa Iran aiki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar rahotanni, dalibin ya ce ya aikata wannan abu ne saboda rashin jin daɗin abin da ƙasar Isra'ila take yi wa falasɗinawa a zirin Gaza.

A ‘yan shekarun nan, Isra’ila ta sha kama wasu mutane da ake zargi da yi wa Iran leƙen asiri, kamar yadda jaridar JNS News ta rahoto.

Isra'ilawa sun faɗi tashin hankalin da suka gani

A wani labarin, kun ji cewa wasu daga cikin mazauna birnin Beersheba da ke Isra'ila sun bayyana irin tashin hankalin da suka shiga lokacin da Iran ta kai masu hari.

Kara karanta wannan

Rufa rufa ta ƙare: An gano mummunan halin da Iran ta jefa Isra'ila bayan tsagaita wuta

Wata mata da ta tsira daga harin ta ce ƙarar lokacin da makami mai linzamin ya faɗo a gidan da ke kusa da su, ya a ta ji kamar mutuwa ce ta tunkaro ta.

Rahotanni sun nuna cewa an samu asarar rayuka a harin wanda Iran ta kai ana dab da fara amfani da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262