"Mun ga Bala'i," Mutanen Isra'ila Sun Fara Faɗin Gaskiya kan Ƙazamin Harin da Iran Ta Kai Masu

"Mun ga Bala'i," Mutanen Isra'ila Sun Fara Faɗin Gaskiya kan Ƙazamin Harin da Iran Ta Kai Masu

  • Wasu daga cikin mazauna birnin Beersheba sun bayyana irin tashin hankalin da suka shiga lokacin da Iran ta kai masu hari a Isra'ila
  • Yahudawan sun bayyana cewa duk da sun gudu sun shiga wuraren da aka gina don kariya, amma ƙarar faɗowar makamin ta gigita su
  • Wata mata mai suna, Merav Manay ta ce ta ɗauka mutuwa ce ta tunkaro su, tana mai cewa harin ya yi masu mummunar illa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Beersheba, Israel - A safiyar Talata, ƙarar jiniyar gargaɗi ta katse barcin mazauna birnin Beersheba a Isra’ila, mintoci kaɗan kafin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Iran da Isra’ila ta fara aiki.

Wani saƙon gaggawa da aka tura ta waya mai taken, “babbar ankararwa” ya ɗaga hankula, kafin kuma jiniya ta fara ƙara da karfi, lamarin ya firgita mazauna birnin.

Kara karanta wannan

Bayan yaƙi da Isra'ila, Shugaba Trump ya faɗi abin da Amurka za ta tunkari Iran da shi

Harin makami mai linzami ya gigita mutanen Isra'ila.
Wasu mazauna Isra'ila sun bayyana tashin hankalin da Iran ta jefa su a ciki Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC Hausa ta tattaro cewa wasu daga cikin mazauna birnin Beersheba sun bayyana irin mummunan halin da suka shiga lokacin da Iran ta jefa makamai kan Isra'ila.

Harin da Iran ta kai Isra'ila ya gigita jama'a

Wata mata, Merav Manay da iyalinta sun ruga zuwa ɗakin tsira da aka gina da siminti mai kauri da ƙofar ƙarfe, domin samun kariya daga hare-haren rokokokin da Iran ta harbo.

Bayan da wani makami daga Iran ya faɗo, Merav ta ce sun ji girgiza sosai har suka ɗora hannu a kai, suna zaton mutuwa ce ta iso.

"Ƙarar ta girgiza duka gidan. Mun ɗauka ƙarshenmu ne ya zo,” in ji Merav.

Bayan sun fito, tagogin gidan sun farfashe gaba ɗaya saboda ƙarfin fashewar, duk da yake babu wanda ya jikkata a gidan nasu.

A ɗaya gefen titin, wani gida makamancin nasu ya ragargaje tare da ƙonewa ƙurmus bayan makamin ya faɗa kai-tsaye a kansa.

Kara karanta wannan

Gaza: An gano yadda mutane 870 suka mutu a kwanaki 12 na yaƙin Iran da Isra'ila

Iran ta kashe mutane 4 a harin

An tabbatar da mutuwar mutum huɗu a wajen. Hukumar tsaron cikin gida ta Isra’ila ta ce su ma waɗanda suka rasu suna cikin ɗakin tsira lokacin da harin ya auku.

Bayan harin, jami’an lafiya da dakarun soji suka isa yankin domin ceto rayuka. Masu aikin sa kai kuma suka fara tona ɓaraguzan gini da suka toshe hanyoyi, rahoton CNN.

Bayan wannan hari ne Iran da Isra’ila suka sanar da amincewarsu da tsagaita wuta. Sai dai bayan sanarwar, kowanne bangare ya fara zargin ɗaya da karya yarjejeniyar.

Iran ta yi barna kafin tsagauta wuta ta fara aiki.
Isra'ilawa sun shiga firgici a harin da Iran ta kai kafin amincewa da tsagaita wuta Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Harin Iran ya ruguza gidajen yahudawa

A yammacin Talata, aka ga wani magidanci, Oren Cohen, da bai wuce shekaru 45, ya tsaya yana kallon gidansa da ya ruahe, yana kusa da gidan da makamin ya faɗa.

“Ina cikin damuwa game da ’ya’yana. Sai yanzu na fahimci girman abin da ya faru,” in ji Oren.

Duk da irin ɓacin ran da ya fuskanta, Oren ya ce yana goyon bayan yaƙin da Isra’ila ke yi da Iran, yana mai cewa, "ba mu da wani zaɓi. Dole ne mu kare kanmu.

Kara karanta wannan

Rufa rufa ta ƙare: An gano mummunan halin da Iran ta jefa Isra'ila bayan tsagaita wuta

Amurka ta shirya ganawa da Iran

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Donald Trump na Amurka ya jaddada cewa yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran ya kare bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Ya ce Amurka za ta gana da jami'an ƙasar Iran domin fara tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa a makon gobe.

Shugaba Trump ya kara nanata cewa Amurka ta yi nasarar lalata shirin nukiliyar Iran, don haka babu sauran wata barazana a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262