Shugaban Chadi Ya Fara Bugawa da Trump, Ya Hana 'Yan Amurka Shiga Kasarsa

Shugaban Chadi Ya Fara Bugawa da Trump, Ya Hana 'Yan Amurka Shiga Kasarsa

  • Chadi ta dakatar da bayar da biza ga 'yan asalin Amurka bayan gwamnatin kasar Amurka ta sanya ‘yan kasar Chadi a jerin takunkumin shige da fice
  • Shugaban kasar Chadi ya bayyana cewa kasar ba ta da jiragen sama ko makudan kudi da za ta ba Donald Trump, amma tana da mutunci da kima
  • Hukumar Tarayyar Afirka ta nuna damuwa kan matakin Amurka, tana kira da a bi hanyar da ta dace wajen yanke irin wannan hukunci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Chad - Chadi ta dakatar da bayar da biza ga 'yan Amurka a matsayin martani kan shigar da 'yan Chadi cikin jerin kasashe 12 da gwamnatin Amurka ta kakabawa takunkumin shige da fice.

Hakan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya hana wasu kasashe 12 shiga Amurka.

Kara karanta wannan

'Tun a tafiya motarmu ke samun matsala,' Yar wasan Kano ta fadi 'dalilin' hadarinsu

Deby ya yi wa Trump martani
Chadi ta hana 'yan Amurka shiga kasarta. Hoto: Donald J. Trump|Mahamat Idriss Deby Itno
Source: Facebook

Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby, ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce matakin ya yi daidai da ka’idar shige da fice tsakanin kasashe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce matakin Chadi na zuwa ne bayan Amurka ta bayyana cewa tana daukar matakin ne don kare 'yan kasarta daga hadarin ta'addanci da barazanar tsaro.

Shugaba Deby ya yi wa Trump martani

Shugaban kasar Chadi ya cire tsoro ya yi wa Donald Trump na Amurka martani kan saka takunkumin tafiye tafiye ga 'yan kasarsa.

A cikin sakonsa, Shugaba Deby ya ce:

"Na umarci gwamnati da ta yi aiki bisa tsarin daidaitawa, ta dakatar da bayar da biza ga 'yan kasar Amurka."

Ya kara da cewa:

"Chadi ba ta da jirage ko makudan kudi da za ta bayar, amma tana da mutunci da kima."

Rahoton Reuters ya nuna cewa kalaman Deby sun biyo bayan kyautar jirgin sama da Qatar ta baiwa shugaban Amurka, Donald Trump.

Kara karanta wannan

Aikin hajji: Saudiyya ta hana maniyyata sama da 200,000 sauke farali

Chadi tana daga cikin kasashen Afirka bakwai da Amurka ta sanya a cikin jerin kasashe 12 da aka kakabawa takunkumi, ciki har da Kongo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia da Sudan.

Dalilin hana 'yan Chadi shiga Amurka

A cewar gwamnatin Amurka, an dauki matakin kakaba takunkumin ne domin kare kasar daga wadanda za su iya aikata ta’addanci ko kuma su kawo barazana ga tsaro da zaman lafiya.

Donald Trump ya hana 'yan Chadi shiga Amurka
Dalilin da ya sa Trump ya hana yan kasashe 12 shiga Amurka. Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Trump ya ce:

“Manufar ita ce kare Amurka daga baki da ke da niyyar aikata ta’addanci ko yada mummunan tunani,”

Gwamnatin Amurka ta kuma ce tana kokarin tantance irin wadannan mutane kafin su samu izinin shiga kasar.

AU ta nuna damuwa kan matakin Trump

Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana damuwa kan yadda Amurka ke daukar matakai marasa hujja da ke iya bata dangantaka mai tsawo tsakanin kasashen Afirka da Amurka.

A cikin wata sanarwa, kungiyar ta ce:

“Muna kira da girmamawa ga gwamnatin Amurka da ta dauki irin wadannan matakai ta hanyar da ta dace,"

Kasar China za ta ziyarci Chadi

A wani rahoton, kun ji cewa ministan harkokin wajen kasar China zai ziyarci wasu kasashen Afrika hudu.

Kara karanta wannan

INSO: Najeriya ta dakatar da kungiyar ketare kan zargin alaka da Boko Haram

Rahotanni sun nuna cewa daga cikin kasashen da zai ziyarta a nahiyar Afrika domin tattauna muhimman abubuwa akwai Chadi.

Legit ta rahoto cewa hakan na zuwa ne bayan shugaban kasar Chadi ya yanke alakar soji da kasar Faransa a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng