Trump Ya Wulakanta Obama, Ya Sauya Hoton Shi a Fadar Amurka
- Fadar White House ta sauya hoton Barack Obama da wani sabon zane da ke nuna Donald Trump bayan yunƙurin kashe shi a wani taro
- Zanen ya nuna lokacin da Trump ya ɗaga hannunsa bayan an harbe shi a kunne, a lokacin da yake yakin neman zaben shugaban kasa
- An ce za a maida hoton George W. Bush kusa da na mahaifinsa, aka matsar da na Obama zuwa bangon da aka saka hoton Bush
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - A ranar Juma’a Fadar White House ta bayyana wani sabon zanen hoton Donald Trump, da aka rataya a babban zauren fadar, wanda ya maye gurbin hoton Barack Obama.
Zanen ya nuna Trump a lokacin da aka kai masa hari a wani taron kamfen a Butler, jihar Pennsylvania, a watan Yuli.

Asali: Twitter
Fadar White House ta wallafa hoton zanen a shafinta na X yayin da aka maye gurbin hoton Obama da na shugaba Trump.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton AP ya nuna cewa zanen ya nuna yadda Trump ya ɗaga hannunsa cikin jini yana ƙarfafa magoya bayansa bayan harbin da ya same shi a kunne.
Trump ya sauya hoton Obama a fadar Amurka
A daidai wurin da aka rataye sabon hoton Trump, hoton Obama ne a wajen tun shekarar 2022 kafin ranar Juma'ar da ta gabata.
Yanzu an matsar da hoton Obama zuwa bangon da hoton George W. Bush ya ke , yayin da na Bush zai koma kusa da na mahaifinsa George H.W. Bush a saman matakala.
Koda yake al’ada ce shugaban kasa mai ci ya gayyaci wanda ya gada domin taron bayyana hotonsa a White House, Trump bai gayyaci Obama ba a lokacin da aka rantsar da shi.
Zanen Trump ya samu karbuwa a Amurka
Wani mai fasaha mai suna Marc Lipp ne ya zana hoton Trump bayan an harbe shi kuma Andrew Pollack ne ya ba da gudumawa sosai wajen zanen.
Ana bayyana Lipp a shafukan yanar gizo a matsayin mai zane na zamani da ya samu karbuwa a duniyar yau.
Pollack da ya ba da gudummawar, shahararre ne wajen fafutukar tsaron makarantu bayan ɗiyarsa ta mutu a wani harin da aka kai wata makaranta a Florida a 2018.

Asali: Twitter
Tasirin hotunan shugabanni a Amurka
Hotunan shugabanni da matayensu suna ɗaya daga cikin abubuwan da dubban baƙi ke gani yayin yawon shakatawa a White House.
Ana rataye su a wurare daban daban ciki har da dakunan tarihi kamar Green Room, Red Room, da kuma State Dining Room.
Sauya hoto da Trump ya yi ya ƙara ƙarfafa ce-ce-ku-ce a siyasar Amurka, musamman a daidai lokacin da aka fara duba yiwuwar sake tsayawarsa takara a 2028.

Kara karanta wannan
'Dan sandan Najeriya ya rasu a gidan kallon ƙwallo ana wasan Arsenal da Real Madrid
Najeriya ta hana shigo da kayan Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta nuna damuwa kan yadda Najeriya ta hana shigo da wasu kayayyakinta.
An hana shigo da kayayyakin ne a lokacin shugaba Muhammadu Buhari domin karfafa 'yan Najeriya su dogara da kansu.
Sai dai Amurka ta ce hakan yana rage yadda 'yan kasuwarta ke samun riba wajen hada hadar kasuwancin tsakanin kasa da kasa.
Asali: Legit.ng