Trump: Amurka Ta Yi Korafi bayan Najeriya Ta Cire Tsoro Ta Hana Shigo da Kayanta
- Gwamnatin Amurka ta caccaki Najeriya bisa haramta shigo da kayayyaki 25, tana mai cewa hakan yana hana ‘yan kasuwarta cin riba sosai
- Wannan martani na zuwa ne mako guda da Donald Trump ya sanya haraji kan kayayyakin da ake shigarwa Amurka, Najeriya ta samu karin 14%
- Ofishin harkokin kasuwancin Amurka (USTR) ya ce dokar da Najeriya ta sanya na haifar da cikas ga cinikayya da rashin samun kudin shiga
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Amurka ta bayyana damuwa kan haramcin da Najeriya ta sanya a kan shigo da wasu kayayyaki 25.
A bayanin da kasar ta fitar, ta bayyana cewa matakin yana tauye damar ‘yan kasuwar Amurka wajen faɗaɗa kasuwanci a Najeriya.

Asali: Facebook
Ofishin kasuwancin Amurka (USTR) ya wallafa a X cewa kayayyakin da aka haramta sun haɗa da nama irin su kaji da alade da shanu, kayan magani da sauransu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
USTR ta ce wannan doka ta hana samun riba da kasuwa ga kamfanonin Amurka, musamman a bangaren noma, magunguna da sauran kayan masarufi.
Kayan da Najeriya ta hana shigowa daga Amurka
Tun a shekarar 2016 ce gwamnatin tarayya ta haramta shigo da wasu kayayyaki domin rage dogaro da kaya daga waje da kuma bunkasa masana’antun cikin gida.
Wasu daga cikin kayayyakin da aka haramta sun hada da dabbobin da aka yanka, man kayan lambu, sukarin rake, koko, taliya, sabulai, tayoyi da aka sake hadawa da sauransu.
A watan Maris, 2025, gwamnatin Najeriya ta kara sanar da shirin hana shigo da kayan sola domin karfafa masana'antun cikin gida.
Najeriya na duba illar harajin gwamnatin Trump
Ministan Kudi da Tsare-Tsaren Tattalin Arziki, Wale Edun, ya ce gwamnati za ta sake nazari kan tasirin harajin da Trump ya kakaba, musamman idan ya dauki lokaci.

Kara karanta wannan
Pascal Dozie: Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da attajirin da ya rasu a Najeriya
A cewarsa, kayayyakin Najeriya ne ke fuskantar karin harajin kashi 14% a Amurka, sai dai hakan bai shafi danyen mai ba, wanda shi ne babban abin da Najeriya ke fitarwa.

Asali: Getty Images
Maganar ministan kasuwancin Najeriya
Ministar Harkokin Kasuwanci, Dr Jumoke Oduwole, ta ce harajin da Trump ya makawa Najeriya na iya kawo barazana ga fitar da kayan noma da na masana’antu.
Ta ce yawancin kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa Amurka – sama da kashi 90% – su ne man fetur da iskar gas, yayin da sinadaran taki ke binsu a baya.
Ta ce harajin da aka ƙara kan wasu kayayyaki na iya raunana kasuwanci da karin matsin lamba kan kananan ‘yan kasuwa da ke fitar da kaya zuwa Amurka.
Amurka ta yi magana kan shari'ar zaben Edo
A wani rahoton, kun ji cewa Amurka ta gargadi Najeriya kan shari'ar da ake yi a kan zaben gwamnan jihar Edo.

Kara karanta wannan
"Najeriya za ta shiga rudani," JNI ta ja kunnen gwamnati kan kisan kiyashi a Filato da Kebbi
A matakan da aka dauka a shari'ar zuwa yanzu, dan takarar jam'iyyar APC da hukumar INEC ta ayyana ya lashe zaben ne ya samu nasara.
Sai dai Amurka ta yi magana kan yadda shari'ar ke gudana, ta ce tana kallon duk abin da yake gudana a gaban kotun sauraron karar zaben.
Asali: Legit.ng