Saudiyya Ta Bayyana Ranar Karamar Sallah bayan Kammala Duban Watan Shawwal

Saudiyya Ta Bayyana Ranar Karamar Sallah bayan Kammala Duban Watan Shawwal

  • Mahukunta a ƙasar Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan Shawwal na shekarar 1446AH wacce ta yi daidai da 2025 na miladiyya
  • An bayyana cewa an ga jinjirin watan Shawwal a yammacin ranar Asabar, 29 ga watan Maris wacce ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan 1446AH
  • Mahukuntan sun bayyana cewa za a gudanar da Sallar idi ta ƙaramar Sallah a ranar Lahadi, 1 ga watan Shawwal 1446AH a ƙasar Saudiyya
  • Sanar da ganin watan na Shawwal na nufin cewa an kawo ƙarshen azumin watan Ramadan na shekarar 1446AH a ƙasa mai tsarki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Saudiyya - Ƙasar Saudiyya ta sanar da ranar ƙaramar Sallah bayan ganin watan Shawwal na shekarar 1446AH.

Mahukunta a Saudiyya sun bayyana cewa gobe Lahadi, ita ce ɗaya ga watan Shawwal 1446AH..

Saudiyya ta sanar da ranar Sallah
Saudiyya ta bayyana ranar karamar Sallah Hoto: @Haramainsharifain
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin sanarwar da aka sanya a shafin Haramain Sharifain na Facebook.

Kara karanta wannan

Bayan soke hawa, Sanusi II ya gana da malaman Musulunci da kusoshin gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana ranar Sallah a Saudiyya

Wannan sanarwar na nufin za a gudanar da ƙaramar Sallah a ranar Lahadi, 1 ga watan Shawwal 1446AH a ƙasa mai tsarki.

Sanarwar ta nuna cewa an kammala azumin watan Ramadan na shekarar 1446AH a Saudiyya bayan an yi guda 29.

Sanarwar ganin watan na Shawwal na cewa:

"Labari da ɗuminsa: Za a gudanar da ƙaramar Sallah (Eid Al Fitr) ta shekarar 1446/2025 gobe Lahadi, 30 ga watan Maris 2025."
"An ga jinjirin watan Shawwal 1446 yau a Saudiyya wanda hakan ke nufin gobe shi ne farkon watan Shawwal 1446."

Sheikh Sudais zai yi limancin sallar idi

Sheikh Abdur Rahman As Sudais ne limamin da zai jagoranci Sallar Idin bana a masallacin Harami da ke birnin Makkah.

Wannan shi ne karo na farko da babban limamin zai jagoranci Sallar Idi a masallacin Harami a cikin shekara 40 da ya yi yana limanci.

Kara karanta wannan

"Za a ga wata yau?": Fadar Sarkin Musulmi ta fitar da sanarwa ana shirin fara duban watan sallah

Da yammacin ranar Asabar ne dai aka fara duba jinjirin watan Shawwal a yankuna da dama na ƙasar Saudiyya.

An ga watan Shawwal a Saudiyya
Saudiyya ta sanar da ganin jinjirin watan Shawwal na shekarar 1446AH Hoto: Haramain Sharifain
Asali: Facebook

Shafin ya bayyana cewa an fara duba jinjirin watan na Shawwal a yankunan Riyadh, Tumair da Sudair.

Tun da farko dai, hankalin masana ganin wata a Saudiyya ya rabu, inda wasu ke.da ra'ayin cewa za a ga jinjirin watan Shawwal a yau Asabar, yayin da wasu ke cewa ba za a gani ba har sai ranar Lahadi.

Karanta wasu labaran kan duba wata

Saudiyya ta turo tallafi ga Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙasar Saudiyya ta aiko da tallafin dabino domin rabawa a wasu jihohin Najeriya.

Kara karanta wannan

Abin ba dadi: 'Yan shi'a sun gwabza da jami'an tsaro, an samu asarar rayuka

Ofishin jakadancin Saudiyya wanda tallafin ya biyo ta hannunsa, ya raba katan-katan na dabino ga gwamnatin jihar Kano da wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Tallafin na dabino.na zuwa ne bayan da al'ummar Musulmi a Najeriya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan na shekarar 1446AH.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng