Shirin Kawo Sabuwar Takardar Kudi a Najeriya da Wasu Kasashe Ya Kankama

Shirin Kawo Sabuwar Takardar Kudi a Najeriya da Wasu Kasashe Ya Kankama

  • Rahotanni na nuna cewa kungiyar ECOWAS ta gudanar da taron majalisar haɗin gwiwar tattalin arziki karo na 11 a birnin tarayya Abuja
  • Ministocin kuɗi da gwamnonin bankunan kasashen sun tattauna kan batun haɗa takardar kudi guda da kuma bunƙasa tattalin arziki
  • Ministan kuɗin Najeriya, Wale Edun, ya jaddada bukatar bin tsarin kudi da kasafin kuɗi domin cimma burin haɗin gwiwar bunkasa tattali

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar ECOWAS na ci gaba da kokarin ƙaddamar da takardar kudi guda da za ta bai wa kasashen yanki damar cin moriyar kasuwanci da tattalin arziki mai ɗorewa.

A taron majalisar haɗin gwiwar tattalin arziki karo na 11 da aka gudanar a Abuja, ministocin kuɗi da gwamnonin bankunan kasashen sun tattauna kan ci gaban Afrika ta Yamma.

Kara karanta wannan

Gwamnatoci sun yi zazzafan martani ga Kiristoci kan rufe makarantu a azumi

Wale Edun
Najeriya za ta cigaba da goyon bayan samar da takardar kudin ECOWAS. Hoto: Wale Edun|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda taron ya gudana ne a cikin wani sako da ma'aikatar kudin Najeriya ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan kuɗin Najeriya, Wale Edun wanda ya jagoranci taron, ya jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da mara wa shirin baya domin tabbatar da nasarar haɗakar tattalin arzikin yankin.

Maganar samar da sabuwar takardar kudi

A yayin taron, ministan kuɗin Najeriya, Wale Edun, ya bayyana cewa Najeriya na aiki tukuru domin cika sharuɗɗan haɗakar kuɗi guda daya a Afrika ta Yamma.

Hakan na zuwa ne yayin da ECOWAS ke ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da ƙaddamar da takardar kudi guda kafin shekarar 2027.

Samar da takardar kudin zai bunkasa tattalin Najeriya da sauran kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS.

Sauye sauyen da aka yi a Najeriya

Wale Edun ya bayyana sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Najeriya ta yi domin habaka tattali a yayin taron.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya fusata, ya nemi a binciki rushe shagunan talakawa 500 a Kano

Ministan ya ce an dauki matakin karya darajar Naira, inganta tsarin haraji, da kuma cire tallafin man fetur, wanda hakan ya taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa.

Bola Tinubu
Shugaban Najeriya kuma shugaban ECOWAS, Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Getty Images

Kalubalen da kungiyar ECOWAS ke fuskanta

Mista Wale Edun ya ce akwai matsaloli da suka hana cimma burin haɗakar tattalin arzikin yammacin Afrika cikin sauri.

Ya ce rashin tsaro, hauhawar farashin kaya, da kuma tasirin matsalolin tattalin arzikin duniya sun hana samun ci gaba cikin lokaci.

ECOWAS na ƙoƙarin taka rawa a duniya

A cewar Edun, haɗin gwiwar ECOWAS da shugabancin G20 na Afirka karkashin Afirka ta Kudu zai taimaka wajen cimma muradun tattalin arziki.

Minsitan ya ce:

"Wannan dama ce ta tsara makomar yankinmu. Dole mu hada hannu domin samar da zaman lafiya, ci gaban tattalin arziki da wadata."

Taron ministocin kuɗi da gwamnonin bankunan kasashen ya nuna cewa akwai bukatar ƙara ƙaimi wajen cimma burin haɗakar tattalin arziki a Afrika ta Yamma.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga matsala, Majalisar Dokoki ta ba shi sa'o'i 48 ya bayyana a gabanta

Tasirin haɗa takardar kuɗi guda ga tattalin arzikin ECOWAS

Haɗa takardar kuɗi guda a yammacin Afirka na daga cikin matakan da kungiyar ECOWAS ke fatan dauka domin saukaka kasuwanci da karfafa tattalin arziki a yankin.

A yayin taron ministocin kudi da gwamnonin bankunan kasashen da aka gudanar a Abuja, an tattauna yadda sabon tsarin kuɗi zai taimaka wajen rage wahalhalun ciniki tsakanin kasashe, kawar da matsalolin canjin kudade, da kuma karfafa haɗin gwiwar kasuwanci.

Wale Edun, ministan kudi na Najeriya, ya jaddada cewa samar da takardar kuɗin zai ba kasashen ECOWAS damar daidaita kudaden musaya, hana faduwar darajar kudaden kasashen daban-daban, da samar da ingantaccen yanayi ga masu saka jari.

Sai dai, akwai kalubalen da ke gaban wannan shiri, musamman rashin tsaro, hauhawar farashin kayayyaki, da kuma matsalolin da tattalin arzikin duniya ke fuskanta.

Duk da haka, ECOWAS na fatan tabbatar da nasarar shirin nan da shekarar 2027, wanda zai kara wa yankin daraja a idon duniya da kuma bai wa kasashen damar samun ci gaba mai dorewa.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: 'Yan Najeriya za su yi tirjiya ga Tinubu kan karin kudin wuta

Darajar Naira na farfadowa a 2025

A wani rahoton, kun ji cewa masana sun fara tattauna dalilan da suka sanya darajar Naira ke kara farfadowa tun da aka shiga shekarar 2025.

Wani masani harkokin kudi ya bayyanawa Legit dalilan da suka sanya kudin Najeriya kara daraja tare da hanyoyin da za a bi wajen tabbatar da dorewar hakan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel