Jirgin Sojoji Ƴa Faɗo kan Gidajen Mutane, Janar da Wasu Sama da 40 Sun Mutu

Jirgin Sojoji Ƴa Faɗo kan Gidajen Mutane, Janar da Wasu Sama da 40 Sun Mutu

  • An rasa rayukan fararen hula da sojoji da wani jirgin yakin sojin Sudan ya faɗo a kan gidaje a wata unguwa a yankin birnin Khartoum ranar Talata
  • Hukumomin kasar Sudan sun tabbatar da cewa mutane da dama sun mutu, wasu kuma sun samu raunuka daban-daban, suna karɓar magani a asibiti
  • Jirgin saman ya gamu da hatsari ne sakamakon tangarɗar na'ura a daidai lokacin da sojojin Sudan ke ci gaba da fafatawa da dakarun kungiyar RSF

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sudan - Wani jirgin yaƙi na rundunar sojojin ƙasar Sudan ya gamu da hatsari bayan ya tashi a wajen birnin Khartoum.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya faɗo ne a unguwar da mutane ke zaune, kuma ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 46 kawo yanzu.

Jirgin sojin Sudan ya faɗo.
Mutane sun mutu da jirgin sojoji ya faɗo kan gidaje a Sudan Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Gwamnatin yankin ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairu, 2026, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun ɓullo da sabuwar dabara, mataimakin ciyaman ya faɗa tarko a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin sojoji ya faɗo kan gidajen jama'a

Jirgin ƙirar Antonov ya faɗo ne a ranar Talata da daddare kusa da tashar soji ta Wadi Seidna da ke Omdurman, daya daga cikin manyan sansanonin sojin kasar Sudan.

Rundunar sojin kasar, wacce ke yakin basasa da dakarun RSF tun watan Afrilu na 2023, ta ce jirgin ya yi hatsari yayin tashinsa, inda ya kashe dakarunta da kuma fararen hula.

Adadin waɗanda suka mutu ya haura 40

A cewar gwamnatin yankin Khartoum, bayan kidaya ta karshe, adadin wadanda suka mutu ya kai 46, yayin da 10 suka jikkata.

Leadership ta rahoto cewa Manjo-Janar Bahr Ahmed, babban kwamanda a Khartoum, yana cikin wadanda suka mutu.

A baya, ma’aikatar lafiya ta kasar, wacce ke da goyon bayan sojoji, ta bayyana cewa mutane 19 ne suka mutu.

Yadda jirgin soji ya rikito kan gidaje

Shaidu sun ce sun ji wata kara mai karfi, sannan gidaje da dama sun ruguje sakamakon hatsarin, sannan kuma.jirgin ya haddasa katsewar wutar lantarki a wasu unguwanni na kusa.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi, ango da yayar amarya sun rasu mintuna 30 kafin ɗaura aure

Ma’aikatar lafiya ta ce an garzaya da wadanda suka jikkata, ciki har da yara, zuwa asibiti mafi kusa.

Me ya haddasa hatsarin jirgin saman?

Wani babban jami’in soja, wanda ya nemi a boye sunansa, ya ce jirgin ya rikito kan gidajen mutane ne sakamakon tangarɗar fasaha da ya samu.

Hatsarin ya faru ne kwana guda bayan da RSF ta yi ikirarin harbo wani jirgin yaki kirar Rasha (Ilyushin) a garin Nyala, babban birnin Darfur ta Kudu.

Rikici tsakanin sojojin gwamnati da RSF yana kara tsananta, musamman bayan da rundunar sojin ta samu nasarori a Khartoum da tsakiyar Sudan.

Sojojin Sudan.
Rundunar sojin Sudan ta rasa dakaru da jirginta ya gamu da hatsari Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jirgin soji ya yi karo na jirgin fasinja

A wani labarin, kun ji cewa wani jirgi mai saukar angulu na sojojin Amurka ya yi taho mu gama da jirgin fasinja na kamfanin American Airlines mai dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata.

Jirgin fasinjojin ya taso ne daga Wichita, Kansas, kuma ya riga ya lula sama a tsayin kimanin kafa 300 lokacin da aka yi taho-mu-gaman.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262