Ajali Ya Yi: Sanata Ta Riga Mu Gidan Gaskiya bayan an Mata Tiyata a Ƙasar Amurka

Ajali Ya Yi: Sanata Ta Riga Mu Gidan Gaskiya bayan an Mata Tiyata a Ƙasar Amurka

  • Sanata Geraldine Thompson daga jihar Florida ta rasu tana zagaye da iyalanta sakamakon tangarɗar da aka samu a aikin gyaran gwiwa
  • Thompson ta fara shiga majalisar dokokin Florida a ranar 6 ga Nuwamba, 2012, inda ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko daga jam’iyyar Democrat
  • Bayan haka, marigayiyar ta ci gaba da zama wakiliyar mazaɓa ta 15 a majalisar dattawan Florida, ta wakilci yankin West Orange County

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Florida, US - Sanata Geraldine Thompson daga jihar Florida ta riga mu gidan gaskiya sakamakon tangarɗar da aka samu bayan an mata tiyata a gwiwa a Amurka.

Iyalan marigayiya sanatar sun tabbatar da rasuwarta a wata sanarwa da suka fitar, sun ce ta mutu ne ranar Alhamis, 13 ga watan Fabrairu, 2025.

Sanata Thompson.
Sanata Geraldine Thompson ta rasu bayan an mata tiyatar gyaran gwiwa a Amurka Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Kamar yadda jaridar AP News ta ruwaito, iyalanta sun ce Sanata Thompson ta rasu ne tana da shekaru 76 a duniya.

Kara karanta wannan

"Wa ya mata cikin?": Jarumar fim a Najeriya ta yi magana kan zargin sanata ya mata ciki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar danginta, za a tuna da ita ba kawai a matsayin shugabar jama’a mai kwazo ba, har ma a matsayin uwa da kakar iyali mai nuna kauna da tausayi ga ƴan uwanta.

Sanarwar ta iyalan Thompson ta ce:

"Sanata Geraldine Thompson ta fi kasancewa shugabar al’umma mai hangen nesa. Ita mace ce da ta sadaukar da kanta ga iyalinta, 'ya'yanta, jikokinta da dukkan al'ummar da take wakilta."

Tarihin siyasar Sanata Thompson

Sanata Geraldine Thompson ta fara aiki a majalisar dokokin jihar Florida da ke ƙasar Amurka tun daga shekarar 2006.

Marigayiyar ta yi aiki a majalisar dokoki ta Florida a tsakanin 2006 zuwa 2012, sannan ta koma sanata a Majalisar dattawa daga 2012 zuwa 2016.

A shekarar 2018 kuma Sanata Thopson ta sake komawa Majalisar dokokin Florida har zuwa shekarar 2022, sannan ta zama sanata a karo na biyu tsakanin 2022 zuwa 2025.

Manyan mutane sun fara alhinin rasuwarta

Kara karanta wannan

Mawaki ya bijirewa mahaifiyarsa, ya koma soyayya da yar majalisa duk da gargadinta

Manyan mutane sun nuna alhinin wannna rashi, ciki har da magajin garin Orange County wanda ya ce za a yi kewarta sosai a siyasar jihar Florida da ke ƙasar Amurka.

Maxwell Frost, wani ɗan siyasa ya bayyana cewa marigayiya Thompson ta taimaki mutane da dama a rayuwarta kuma ciki har da shi.

Magajin garin Orange County, Jerry Demings ya nuna alhini da wannan rashi, yana mai cewa:

"Ta kasance mai fafutukar kare hakkin mabukata, kuma za a ji rashinta a siyasar Florida."

Haka nan kuma wakiliyar Majalisa, Anna Eskamani ta ce:

"Ko da kuwa ta kawo kudirorin da ƴan Majalisa ba su goyon bayanta a kai, duk suna mutuntata kuma suna sauraron ta lokacin da take magana."
"Za a ci gaba da tuna da irin gudunmawar da ta bayar ga al’ummarta da siyasar jihar Florida. Wannan babban rashi ne a siyasarmu."

Kotu ta ɗaure sanata a Amurka

Kara karanta wannan

Tsagwaron son zuciya ya sa malamin addini kashe dalibar da ya hadu da ita a Facebook

A wani labarin, kun ji cewa tsohon sanata a ƙasar Amurka, Bob Menendez zai shafe shekaru 11 a gidan kaso bayan kotu ta yanke hukunci kan tuhumar cin hanci.

Tun farko masu kara sun nemi a yanke masa hukuncin shekaru 15, saboda a cewarsu cin hanci da rashawa babban laifi ne a ƙasar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262