Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji Ya Ɓace a Sararin Samaniya, An Neme Shi an Rasa
- Hukumomi sun fara binciken wani jirgin sama na haya wanda ya ɓace bayan ya tashi daga Unalakleet zuwa Nome a ƙasar Amurka
- An ruwaito cewa jirgin na ɗauke da mutane tara da matuƙi ya ɓace ne da yammacin ranar Alhamis kafin ya isa garin da ya dosa
- Hukumar kashe gobara ta jihar Alaska ta bayyana cewa jami'an agaji sun ƙara ƙaimi wajen lalubo jirgin saman duk inda ya maƙale
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Hukumomi a jihar Alaska da ke ƙasar Amurka na ci gaba da bincike domin gano wani karamin jirgin haya da ya bace dauke da mutum goma.
Jirgin Bering Air Caravan, dauke da fasinjoji tara da matuki guda, ya tashi daga Unalakleet zuwa Nome da misalin karfe 4:00 na yamma agogon Alaska (01:00 GMT) a ranar Alhamis.

Source: Getty Images
Ƴan sandan jihar Alaska sun bayyana cewa har kawo yanzu jirgin bai isa inda ya nufa ba, kamar yadda jaridar Sky News ta rahoto.
Tazarar da ke tsakanin Unalakleet wurin da jirgin ya taso da Nome ya kai kusan kilomita 235 (mil 146) a yammacin jihar Alaska, kusa da Norton Sound.
Yadda jirgin sama ya ɓace a sama a Amurka
Hukumar kashe gobara ta Nome ta ce matukin jirgin ya sanar da masu kula da tafiyar jirgi a Anchorage cewa zai tsaya a sama yana shawagi har sai an gyara hanyarsa ta sauka, daga nan ba a ƙara jin labarinsa ba.
Hukumar ta kara da cewa rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Amurka ta tura jirgin C-130 domin taimakawa hukumomin bincike wajen gano wurin da jirgin yake.
A sabon bayani da aka fitar a ranar Juma’a, hukumar ta ce:
"Har yanzu ba mu da sababbin bayanai kan wurin da jirgin yake. Hukumomin bincike na ci gaba da kokarin gano shi, suna duba yankunan da ya kamata."
Wurin da aka ji ɗuriyar jirgin na ƙarshe
Jirgin ya aika da sakon matsayarsa na karshe a saman ruwa, kimanin minti 40 bayan tashinsa.
Wannan ba shi ne karon farko da hatsarin jirgin sama ke faruwa a Amurka ba a 'yan kwanakin nan.
A ranar 30 ga Janairu, wani jirgin fasinja ya yi karo da jirgin helikwafta na sojin Amurka a birnin Washington, inda duka mutane 67 da ke ciki suka rasa rayukansu.
Bayan wannan kuma, wani jirgin daukar marasa lafiya ya fado a unguwar da ake cunkoson jama’a a Philadelphia, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai da jikkata 19.
A halin yanzu, ana ci gaba da kokarin gano inda jirgin da ya bace a Alaska yake, tare da fatan samun nasara a binciken.
Jirgin sama ya fado a kasar Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa wani karamin jirgin sama ya rufto ƙasa a Arewa maso Gabashin birnin Philadelphia ta ƙasar Amurka a ranar Juma'a da ta gabata.
Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta Amurka (FAA) ta tabbatar da cewa akwai mutane shida a cikin jirgin na Learjet.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng


