Tsohon Sanata Ya Zubar da Hawaye da Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Daurin Shekaru 11
- An yanke wa tsohon Sanata Bob Menendez hukuncin shekaru 11 a gidan yari bisa laifin cin hanci da rashawa a ƙasar Amurka
- Kotu ta umarci ƙwace dukiyar haram da ya mallaka da darajarta ta kai $992,188.10 duk da rokon da ya yi wa alkali har da zubar da hawaye
- Menendez ya sha alwashin ɗaukaka ƙara kuma ya nemi afuwar Donald Trump, bayan ya kasa samun afuwa daga tsohon shugaba Joe Biden
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Kotu a ƙasar Amurka ta yankewa tsohon Sanata Bob Menendez na New Jersey hukuncin ɗaurin shekaru 11 a gidan yari.
A hukuncin da ta yanke ranar Laraba, 29 ga watan Janairu, 2025, Kotun ta ɗaure tsohon sanatan ne bayan samun shi da laifin cin hanci da rashawa.

Asali: Facebook
Masu gabatar da kara sun nemi a yanke masa hukuncin shekaru 15, suna mai jaddada "girman laifuffukan" da tsohon sanatan ya aikata, cewar rahoton CNN.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane laifi tsohon sanatan ya aikata?
A shekarar da ta gabata, an kama Menendez da aikata laifuka 16, ciki har da karɓar kyaututtuka kamar sandunan zinare, kuɗi, da motar Mercedes-Benz.
An gano cewa tsohon sanatam ya samu waɗannan kyaututtuka ne a matsayin ladan taimakawa gwamnatocin ƙasashen Masar da Qatar.
Menendez, mai shekaru 71, ya roƙi alƙalin kotun tarayya, Sidney Stein, da ya taimaka ya masa sassauci, jaridar AP News ta tattaro.
Tsohon sanata ya zubar da hawaye a kotu
Kuma rahotannni sun nuna cewa har sau biyu yana zubar da hawaye, yana cewa, "Na rasa komai."
Har ila yau lauyoyinsa sun roki kotun da ta tausaya masa, ta masa hukunci ɗan ƙarami, ka da ya shafe shekaru da yawa a gidan gyaran hali duba da hidimar da yi yi wa al'umma.
Duk da haka, alƙalin ya yanke masa hukuncin shekaru 11 a gidan yari, tare da umarnin ƙwace duk wasu dukiyoyin da ya samu ta haram.

Kara karanta wannan
Jikin tsohon gwamnan Taraba ya rikice, kotu ta ba shi damar neman lafiya, an tono barnarsa
Kotu ta kwace duka dukiyoyinsa na haram
Dukiyoyin da kotun ta ba da umarnin kwacewa daga hannun tsohon sanatan sun kai $992,188.10, a cewar ofishin lauyan tarayya na ƙasar Amurka.
Menendez ya yi alkawarin ɗaukaka ƙara, kuma ya nemi afuwa daga Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump bayan kasa samun afuwa daga tsohon shugaban da ya sauka, Joe Biden.
Ya kuma aro kalaman da Trump ya riƙa faɗa kan shari'ar da ake masa kafin ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, inda ya yi ikirarim cewa ya faɗa tarkon 'farautar siyasa'.
Amurka za ta dawo da ƴan Najeriya 5,144 gida
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya fara koro baƙi, za a dawo da ƴan Najeriya 5,144 gida.
An ruwaito cewa galibin wadanda abin ya shafa sun aikata laifuffuka ne daban-daban, wasu kuma sun karya dokokin shige da fice yayin zamansu a Amurka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng