Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji Ya Yi Taho Mu Gama da Jirgin Sojoji, An Rasa Rayuka

Jirgin Sama Ɗauke da Fasinjoji Ya Yi Taho Mu Gama da Jirgin Sojoji, An Rasa Rayuka

  • Wani jirgin saman fasinjoji da helikwaftan rundunar sojojin Amurka sun yi taho mu gama a babban birnin kasar watau Washington DC
  • Jirgin saman na kamfanin American Airlines ya gamu da wannan hatsari ne bayan ya taso daga Wichita, mutum 18 sun mutu kawo yanzu
  • Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa ya samu labarin faruwar hatsarin kuma ya yabawa jami'an da suka kai ɗauki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Washington DC - Wani jirgin fasinja na kamfanin American Airlines mai dauke da fasinjoji 60 da ma’aikata hudu ya yi karo da wani helikwafta na sojojin Amurka.

Jirgin sojojin kirar Black Hawk mai dauke da sojoji uku da jirgin fasinjojin sun yi taho mu gama ne a kusa da birnin Washington DC, Amurka.

Jirgin sama.
Jirgin Sama dauke da fasinjoji ya ci karo da jirgin sojoji a ƙasar Amurka Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wani jami’in soja ya bayyana cewa helikwaftan hukumar sojin ya fito atisaye ne lokacin da hatsarin ya faru, kamar yadda BBC News ta tattaro.

Kara karanta wannan

Bayan abin da ya faru a filin jirgin Kano, NCAA ta dakatar da kamfanin Max Air

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiragen sama 2 sun yi taho mu gama

Jirgin American Eagle Flight 5342 wanda ya ɗauko fasinjoji 60 yana kan hanyarsa zuwa filin jirgin saman Ronald Reagan Washington a daren Laraba lokacin da hatsarin ya afku.

Jirgin ya taso ne daga Wichita, Kansas, kuma ya riga ya lula sama a tsayin kimanin kafa 300 lokacin da aka yi taho-mu-gama, a cewar NBC News..

Kamfanin jirgin fasinjan ya tura tawaga

Shugaban kamfanin American Airlines, Robert Isom, a cikin wani sakon bidiyo ya ce zai tafi wurin da hatsarin ya afku tare da wata tawagar kamfanin nan ba da jimawa ba.

"A yanzu hankalinmu na kan fasinjoji da ma'aikatan da ke cikin jirgin, muna aiki tare da hukumomi kuma za mu ba da duk gudummuwar da ake bukata a aikin ceto."

Wannan hatsari yana daya daga cikin munanan hadurran jirgin sama da suka afku a Amurka cikin sama da shekaru 15.

Kara karanta wannan

Max Air ya fitar da bayanai a kan hatsarin jirginsa a Kano, an rufe titin saukar jirage

Mutum 18 sun mutu kawo yanzu

Yanzu haka dai jami'ai na ci gaba da ayyukan ceto da neman wadanda lamarin ya rutsa da su a kogin Potomac wanda ke kusa da wurin da hatsarin ya afku.

Jami'an 'yan sanda sun sanar da cewa an gano gawarwaki 18, amma babu wani bayani a hukumance game da asarar rayuka.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya samu labarin faruwar lamarin, tare da gode wa masu aikin ceto bisa "aikin ban mamaki" da suke yi.

Jirgin sama ya faɗo a ƙasar Brazil

A wani labarin, kun ji cewa jirgin sama da ya ɗauko fasinjoji sama da 60 ya gamu da mummunan hatsari a kusa da birnin Sao Paulo na ƙasar Brazil.

Rahotanni daga kasar Brazil sun nuna cewa duka fasinjoji 62 da jirgin ya ɗauko sun mutu sakamakon hatsarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel