Ta Faru Ta Kare: Kasashen Afrika 3 Sun Fice daga ECOWAS duk da Sa Bakin Tinubu

Ta Faru Ta Kare: Kasashen Afrika 3 Sun Fice daga ECOWAS duk da Sa Bakin Tinubu

  • ECOWAS ta sanar da ficewar kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar daga kungiyar, bayan sun janye daga cikin ta a shekarar da ta gabata
  • Kasashen uku sun kafa Kungiyar Kasashen Sahel, tare da kaddamar da fasfo nasu bayan dogon lokaci ana ja-in-ja da su a tafiyar ECOWAS
  • ECOWAS ta ba da wa’adin wata shida don sake tunani game da ficewar kasashen, yayin da ake ci gaba da tattaunawa don warware rikicin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - ECOWAS ta sanar da cewa Mali, Burkina Faso da Nijar sun fice daga kungiyar bayan sun janye daga cikin ta a shekarar da ta gabata.

A cikin shekaru biyar da suka gabata, Yammacin Afrika ta gamu da juyin mulkin soja a wasu daga cikin kasashen ECOWAS 15.

ECOWAS ta yi magana da Burkina Faso, Mali da Nijar suka ficewa daga kungiyar a hukumance.
Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga ECOWAS a hukumance. Hoto: @GoitaAssimi
Asali: Twitter

ECOWAS ta sanar da ficewar su Burkina Faso

Kara karanta wannan

Yankunan Najeriya da suka fi samar da harajin VAT da yawan kudin da aka tatsa a 2024

A sanarwar da ECOWAS ta fitar a shafinta na X a ranar Laraba, 29 ga watan Janairun 2025, kungiyar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ficewar Burkina Faso, Jamhuriyar Mali da Jamhuriyar Nijar daga ECOWAS ta fara aiki daga yau, 29 ga Janairu 2025."

Wadannan kasashe uku sun sanar da ficewarsu daga kungiyar a watan Janairun bara bayan ECOWAS ta nemi dawo da mulkin dimokaradiyya a Nijar.

Maimakon haka, kasashen uku sun kafa Kungiyar Kasashen Sahel, wata kungiya mai zaman kanta kuma sun kaddamar da fasfo nasu.

Kasashen 3 sun kafa kungiyar Sahel

A ranar Labara, ECOWAS ta ce sauran mambobinta sun amince da barin kofar ECOWAS a bude ta hanyar amincewa da fasfo, nau'in shaidar zama da kansa daga kasashen uku.

Kungiyar ta nemi sauran mambobinta da su ci gaba da mutunta al'ummar wadannan kasashe uku, musamman ta hanyar ba su damar shige da fice da kasuwanci.

A watan Disamba, ECOWAS ta ba Mali, Burkina Faso da Nijar wa'adin wata shida don su sake tunani game da ficewarsu, wa'adin da bai canja ra'ayin nasu ba.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

ECOWAS ta ce:

"Wannan shirye-shiryen za su kasance har zuwa lokacin da za a kammala nazarin yadda alaka za ta ci gaba da kasancewa da kasashen uku."

Zanga zanga a kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso

An kafa kungiyar ECOWAS a shekarar 1975, tare da kasashe 15, domin ta yi aiki a matsayin jagorar siyasa a yankin, ta kuma yi aiki tare da kasashe.

Sai dai kungiyar ta yamutse lokacin da aka samu juyin mulki a wasu kasashen cikinta, da kuma tashe tashen hankula da ma rikici kan tasirin Rasha da Faransa.

Dubban mutane sun fito ranar Talata a Nijar da Burkina Faso don goyon bayan wannan matakin na ficewa daga ECOWAS.

A Nijar, jagororin gwamnatin sojoji a babban birnin Niamey sun jagoranci zanga-zangar kin goyon bayan Shugaban Faransa Emmanuel Macron.

A Burkina Faso, dubban mutane, ciki har da Firaministan Rimtalba Jean-Emmanuel Ouedraogo, sun taru a dandalin kasa na Ouagadougou.

Kara karanta wannan

Wata tankar man fetur ta sake fashewa a jihar Neja, ana fargabar mutane sun mutu

"Don yanke dangantaka da mulkin mallaka... wannan ba za'a yi shi da hannun mai karbar haihuwa ba, sai dai da kaifin takobi," inji Ouedraogo.

Bayan samun mulki a cikin shekaru biyar da suka gabata, shugabannin sojojin a wadannan kasashe sun zargi ECOWAS da nuna sha'awar Faransa.

Tinubu ya fadi shirunsu a kan Nijar da Mali

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana matakan da ECOWAS ke ɗauka don shawo kan Nijar, Mali da Burkina Faso su koma cikin ƙungiyar.

Tinubu, wanda shi ne shugaban ECOWAS, ya bayyana hakan yayin ganawarsa da Shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, a birnin Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.