An Farmaki Fitaccen Jarumin Fina Finai a cikin Gidansa, An Kwantar da Shi Asibiti
- Wani dan ta'adda ya shiga gidan jarumi Saif Ali Khan da tsakar dare, inda ya daba masa wuka yayin da suka gwada kwanji
- ‘Yan sanda sun fara bincike kan wanda ya kai wa Saif Ali Khan hari, yayin da aka tabbatar da lafiyarsa bayan yi masa tiyata
- Wannan lamarin ya jefa iyalin Saif Ali Khan a cikin tsananin firgici yayin da yake ci gaba da samun kulawa daga likitocinsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Mumbai - An yi nasarar yiwa fitaccen jarumin Bollywood Saif Ali Khan tiyata bayan wani dan ta'adda ya daba masa wuka a gidansa.
An ce dan ta'addan ya kai harin ne da sanyin safiyar Alhamis a wata unguwar masu kudi da ke Mumbai, inda Saif Ali Khan ke zaune tare da iyalinsa.

Asali: Twitter
Dan ta'adda ya farmaki jarumin Bollywood
Rundunar ‘yan sandan Mumbai ta shaida wa BBC Marathi cewa jarumin ya ji rauni bayan fada tsakaninsa da wanda ya shiga gidansa da tsakar dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda sun kafa kwamitoci don gudanar da bincike kan lamarin.
"An fito da Saif Ali Khan daga tiyata kuma yana cikin koshin lafiya. Yanzu haka yana samun kulawa yayin da likitoci ke bibiyar yanayinsa."
- Inji tawagar jarumin.
Likita ya fadi aikin da aka yi wa Saif Ali Khan
Da yake magana da manema labarai, Dakya Nitin Dange na asibitin Lilavati ya ce Saif Ali Khan ya ji mummunan rauni a kashin baya.
"An yi tiyata don cire wukar kuma an gyara jijiyoyinsa. Haka kuma, an gyara raunuka masu zurfi a hannunsa da wuyansa," inji likitan.
Iyalan Saif Ali Khan da suka hada da matarsa, jarumar Bollywood Kareena Kapoor Khan, wadda suka haifi yara biyu ba su fitar da wata sanarwa ba tukuna.

Kara karanta wannan
Jirgin Max Air da ya tashi daga Legas zuwa Kano ya yi hatsari, an samu karin bayani
'Yan sanda sun yi bayani kan harin
Cikakkun bayanai kan harin ba su fito fili ba har yanzu amma ‘yan sanda sun ce yi karin bayani kan yadda aka kai farmakin.
"Mutumin da ba a san ko wanene ba ya shiga gidan Khan. Daga nan ne fada ya barke tsakanin Khan da mai kai harin."
- A cewar kwamishinan ‘yan sandan Mumbai, Dixit Gedam.
Tawagar Khan ta ce sun kyautata zaton an kai harin ne da nufin yin sata, amma dai tawagar ba ta bayar da karin bayani a kai ba.
"Muna rokon kafafen yada labarai da masoya su dan jira tukunna. Wannan al'amari ne na ‘yan sanda," inji tawagar jarumin.
Wanene jarumi Saif Ali Khan?
Saif Ali Khan ya fara fitowa a finafinan Bollywood a 1993, ya fi shahara wajen fina-finai masu ban dariya da kuma wasan kwaikwayo.
Daga cikin fina-finansa akwai Dil Chahta Hai, Kal Ho Naa Ho, Tanhaji, da Devara: Part 1.
A shekarar 2006, tauraruwar Saif Ali Khan ta sake haskawa bayan rawar da ya taka a fim din Omkara na Shakespeare.
Khan ya fito daga dangin Sarakunan Pataudi kuma ya shiga ahalin jarumai ta hanyar aure.
Mahaifinsa Mansoor Ali Khan Pataudi tsohon dan wasan cricket ne kuma mahaifiyarsa Sharmila Tagore tsohuwar jaruma ce.
‘Yar uwarsa Soha Ali Khan ta yi fim na wani lokaci yayin da matarsa Kareena Kapoor Khan ta fito daga dangin jarumai da aka dade ana damawa da su a Bollywood.
An dakatar da 'yar wasar fim
Idan aka dawo gida, ana da labari hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta dakatar da Samha M Inuwa saboda yaɗa baɗala.
Hukumar ta bayyana 'yar wasar ta yi kunnen uwar shegu da jan-kunnenta kuma ta sha alwashin ci gaba da tsabtace masana'antar ta Kannywood daga munanan ɗabi'u.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng