Shugaban Ghana Ya Jefa Mutanen Duniya a Mamaki wajen Kiran Tinubu a Taro
- Sabon shugaban Ghana, John Mahama, ya yi kuskuren kiran shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a matsayin shugaban Ghana yayin rantsarwarsa
- Yayin jawabinsa a wajen taron, Bola Tinubu ya tabbatar wa Mahama cewa Najeriya za ta ci gaba da bayar da gudunmawa domin ci gaban Ghana
- Shugaba Tinubu ya yaba da hadin kai da ci gaban dimokuradiyya da ake samu a kasashen Afirka, musamman a Yammacin nahiyar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ghana - A wani abin mamaki yayin bikin rantsarwa, sabon shugaban Ghana, John Mahama, ya yi kuskuren kiran shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin shugaban Ghana.
Kuskuren ya faru ne yayin da Mahama ke gabatar da jawabin rantsarwa a gaban taron jama’a da manyan baki daga kasashen Afirka da suka hallara Accra, babban birnin Ghana.
The Cable ta wallafa cewa Bola Tinubu ya amsa kuskuren cikin murmushi, yana mai jaddada muhimmancin hadin kai da goyon bayan Najeriya ga Ghana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kuskuren Mahama wajen kiran Tinubu
A jawabin da ya yi a wurin taron, Mahama ya jinjina wa mambobin majalisar kasar, mataimakiyar shugabar kasa, Jane Naana Opoku-Agyemang, shugaban alkalan Ghana.
Bayan haka sai ya ce;
"Ina jinjinawa mai girma Bola Ahmed Tinubu, shugaban Tarayyar Ghana, wanda kuma shi ne babban bako na musamman a wannan bikin.”
Kuskuren ya jawo dariya da mamaki daga jama’a, amma Mahama bai gyara maganarsa ba har zuwa karshen jawabinsa.
Najeriya za ta cigaba da hada kai da Ghana
Da yake mayar da martani a jawabinsa, shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa sabon Shugaban Ghana cewa Najeriya za ta ci gaba da bayar da tallafi domin ci gaban kasarsa.
“Ina nan ba kawai a matsayin shugaban tarayyar Najeriya ba, har ma a matsayin dan Afirka da ke tare da Ghana da mutanenta.
"Wannan rana wata babbar abin alfahari ce ba wai ga 'yan Ghana ba kadai, har ma ga duk 'yan Afirka.”
- Bola Tinubu
Tinubu ya yaba wa Mahama a matsayin shugaba mai kishin kasa, tare da jaddada cewa gwamnatinsa za ta kawo cigaba da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.
Ya kara da cewa;
“Ni da Mahama muna da kyakkyawar alaka. Na tabbata cewa zai kasance shugaban da zai ciyar da Ghana gaba.
Najeriya za ta kasance tare da Ghana a kowane lokaci da aka bukaci goyon bayanmu.”
Hadin kai da dimokuradiyya a Afirka
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa nasarorin da aka samu a bangaren dimokuradiyya a kasashen Yammacin Afirka, musamman Ghana da Najeriya.
Ya ce zabe irin na Mahama da na sauran shugabannin Ghana ya nuna cewa a Yammacin Afirka muna da kwarewa wajen gudanar da dimokuradiyya mai inganci.
Tinubu ya kuma yi kira ga shugabannin Afirka su guji barin masu sukar nahiyar su bata musu suna.
Ya ce lokaci ya yi da za mu mayar da hankali kan ci gabanmu maimakon mayar da hankali kan ra’ayoyin marasa kishinmu.
Hajjin bana: Abba ya yi kira ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rage kudin aikin Hajji.
Mai girma Abba Kabir Yusuf ya yi jawabin ne a Kano yayin wani taron hukumar alhazai inda ya ce hakika ana cikin matsin tattalin arziki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng