"Da Sanin Najeriya": Shugaban Nijar Ya Magantu kan Shigo da Lakurawa

"Da Sanin Najeriya": Shugaban Nijar Ya Magantu kan Shigo da Lakurawa

  • Shugaban soja na jamhuriyyar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya zargi hukumomin Najeriya da kokarin cutar da Nijar
  • Ya bayyana cewa 'yan ta'addan Lakurawa da ke wasu sassan Arewacin Najeriya shiri ne na musamman domin cutar da ita
  • Abdourahamane Tchiani ya ce bayan sun sanar da hukumomin Najeriya wannan mummunan shiri ne su ka samu labarin Najeriya na sane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jamhuriyyar Nijar - Shugaban soja na kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya zargi gwamnatin Najeriya da hannu dumu-dumu a wajen cutar da ita.

Shugaban ya ce 'yan ta'addan Lakurawa da aka zuba a wasu sassan Najeriya wani kulli ne tsakanin kasar Faransa da 'yan ta'addan ISWAP.

Nijar
Nijar ta zargi Najeriya da yi mata makarkashiya Hoto: Najib Lawal
Asali: Facebook

A wata hira da ta kebanta da TRT Hausa, Janar Abdourahamane Tchiani ya fusata a kan yadda makwabciyarta Najeriya ta san da shirin amma ta yi gum.

Kara karanta wannan

"Akwai kullin arziki a 2025," Ganduje ya nemi a kara yi wa Tinubu uziri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Nijar da san da 'shirin' Faransa

Shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani ya bayyana cewa sun kama wasu daga cikin 'yan ta'addan Lakurawa da su ka ba su muhimman bayanan ayyukansu.

A cewar Janar Tchiani;

"Su ka ce mana to, akwai wata shawara da ake yi, amma shugabannin Najeriya sun san da ita, shi ne akwai wani daji da ake cewa gaba, gaba nan wajen Sakkwato, dajin nan ana so a maida shi tsibiri ne na 'yan ta'adda wanda ake cewa Lakurawa."

Nijar ta sanar da Najeriya shirin Faransa

Shugaban jamhuriyyar Nijar ya bayyana cewa ISWAP da Faransa sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya a ranar 4 Maris, 2024 domin tabbatar da kirkirar 'yan ta'addan Lakurawa.

Ya ce sun yi kokari wajen sanar da gwamnatin Najeriya, har aka gayyato jagororin kasar zuwa Nijar har sun tattauna da Lakurawan da aka kama, amma sun gano kasar nan ta san da batun.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda suka kama miyagu 30,313 da bindigogi 1,984 a 2024

Sojoji sun yi kuskuren kai hari kan ƙauyuka

A baya mun wallafa cewa dakarun sojojin sama na Najeriya su ka yi kuskure a wajen kai wa 'yan ta'addan Lakurawa hari a Sakkwato, inda su ka hallaka mazauna wani kauye.

Rahotanni sun bayyana cewa an jefa bama-baman a kan wasu bayin Allah da ke wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Silame tare da kashe mutane akalla 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel