Alaka Ta Kara Tsami, Nijar Ta Zargi Tinubu da Neman Kassara Ta, Ta Gano Makarkashiyarsa

Alaka Ta Kara Tsami, Nijar Ta Zargi Tinubu da Neman Kassara Ta, Ta Gano Makarkashiyarsa

  • Kasar Nijar ta nuna damuwa kan yadda Najeriya ke cigaba da neman kawo tarnaki ga gwamnatin sojoji a kasar
  • Ministan harkokin wajen kasar, Bakary Yaou Sangare ya zargi Najeriya da hada baki da wasu ƙasashe domin kawo musu cikas
  • Hakan na zuwa ne tun bayan kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum da sojoji suka yi a shekarar 2023 da ta gabata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Niamey, Nijar - Ministan harkokin wajen Nijar, Bakary Yaou Sangare ya gayyaci jakadan Najeriya da ke kasar kan wata barazana da suka hango.

Bakary Yaou Sangare ya zargi Najeriya da taimakawa wajen shirya yunkurin da zai kawo tarnaki ga mulkin sojin da ke jagorantar Nijar.

Nijar ta gargadi Najeriya kan shiga lamarin mulkinta
Nijar ta zargi Najeriya da neman kawo mata tsaiko a tsarin mulkinta. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Alaka ta kara tsami tsakanin Najeriya da Nijar

Tribune ta ce hakan bai rasa nasaba da kokarin shugaban kasa, Bola Tinubu na ƙoƙarin dawo da hambararren shugaban Nijar, Mohamed Bazoum a baya.

Kara karanta wannan

Ana jimamin mutuwar yara 35 a wurin nishaɗi, ibtila'i ya sake afkawa mutane a Ibadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidan Talabijin na kasar Nijar ya bayyana wannan labari a ranar Alhamis 19 ga watan Disambar 2024.

Lamarin ya kara rura wutar rashin jituwar da ke tsakanin kasashen makwabta da juna tun bayan kifar da gwamnatin Bazoum.

Rikicin ya samo asali ne daga juyin mulki na shekarar 2023 a Nijar, wanda ya katse huldar kasar da Kungiyar ECOWAS.

Nijar ta zargi Tinubu da hade musu baki

Minista Sangare ya nuna bacin ransa kan abin da ya kira 'kokarin da Najeriya ke yi da nufin kawo barazana ga kasar'.

“Duk da kokarin farfado da huldar diplomasiyya, muna bakin cikin cewa Najeriya ba ta daina zama wata mafaka ga wadanda ke kokarin haddasa rikici a Nijar ba."
"Hakan na zuwa tare da goyon bayan wasu kasashen waje da kuma jami’an tsohon shugaban kasa da suke samun mafaka a Najeriya."

- Bakary Yaou Sangare

Dakarun Nijar sun hallaka yan kungiyar Lakurawa

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

Kun ji cewa Rundunar sojin Nijar ta tabbatar da kashe mayakan Lakurawan da su ka kutsa kasar a samame da suka kai a yankin Illela na jihar Tahoua.

An samu rahoton cewa sojojin Najeriya sun fatattaki Lakurawan, inda su ka tsallaka cikin Nijar bayan sun kasa jure harin dakarun kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.