Jerin Kasashen Afirka 6 da Suka Datse Alaka ko Suka Fatattaki Sojojin Faransa
A ƴan makonnin nan an yaɗa raɗe-raɗen cewa gwamnatin tarayya ta gayyato sojojin ƙasar Faransa domin su taimaka wajen yaƙi da ƴan tada ƙayar baya.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Jita-jitar kafa sansanin sojojin Faransa a Najeriya ta haddasa cece-kuce, inda manyan mutane da Malamai suka nuna rashin gamsuwa da matakin.
Amma hedkwatar rundunar sojin Najeriya watau DHQ ta musanta batun kawo sojojin Faransa, inda ta ce rahoton ba shi da tushe balle makama, rahoton Punch.
Kasashen Afirka sun katse alaka da sojin Faransa
A baya-bayan nan ne kasashen Afirka da dama suka dauki matakin kawo karshen tasirin soja da siyasar ƙasar Faransa a faɗin iyakokinsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana ganin ƙasashen sun ɗauki wannan matakin ne da nufin kawo karshen mulkin mallaka da kuma daƙile katsalandan ɗin da Faransa take yi a harkokinsu na cikin gida.
Shekaru da dama da suka wuce, ana kallon sansanonin sojin Faransa da aka kafa a kasashen Afirka a matsayin ginshiƙi da dabarun haɗin gwiwa.
A wannan babin, Legit Hausa ta tattaro maku ƙasashen Afirka da suka yi fatali da yarjejeniyar tsaro da Faransa ko ma suka kori sojojin ƙasar gaba ɗaya.
1. Nijar ta yanke alaƙa da sojin Faransa
Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar ta katse duk wata alaƙa da taimakon soji da ƙasar Faransa a 2023, cewar rahoton Africa Insider.
Sojojin da suka karɓi mulki a Nijar sun haramtawa kungiyar agaji ta Faransa ci gaba da gudanar da harkokinta a kasar tare da soke lasisi ba tare da bayani ba.
Haka nan kuma sun kori jakadan Faransa da ke Nijar, lamarin da ya kara dagula alaka tsakaninsu da Faransa.
Faransa ta nuna damuwa da matakin gwamnatin sojin Nijar na aiwatar da irin wadannan hukunce-hukuncen, lamarin da ya kara tada jijiyoyin wuya.
2. Ƙasar Chadi ta katse yarjejeniyar haɗin guiwa
Chadi ta kawo karshen yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da Faransa, da nufin tabbatar da 'yancin kai da kuma daidaita kawancenta kasashen duniya.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, Abderaman Koulamallah ya bayyana hakan a matsayin wani sauyi mai cike da tarihi.
BBC ta kawo rahoto cewa ƙasar Chadi ta soke yarjejeniyar tsaro da Faransa ne shekaru 60 bayan samun 'yancin kai.
3. Gabon ta raba gari da sojin Faransa
A ranar 30 ga watan Agustan 2023 ne sojojin Gabon suka kwace mulki, inda suka tsare shugaban kasar, Ali Bongo Ondimba a fadarsa jim kadan bayan ya ci zaɓe a karo na uku.
Daga baya aka nada Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya.
A watan Satumba, Ministan Sojin Faransa Sébastien Lecornu ya sanar da dakatar da hadin gwiwar soji da sabuwar gwamnatin Gabon bayan juyin mulkin, in ji rahoton RFI.
4. Haɗin guiwar Mali da sojin Faransa ta ƙare
Kawancen Faransa da da gwamnatin sojin Mali na yaki da ƴan tada kayar baya ya rushe bayan juyin mulkin sojoji sau biyu a 2020 da 2021.
Rashin sanya wa'adin miƙa mulki ga fararen hula da zargin tsoma bakin Faransa a harkokin Mali ya ƙara sa alaƙar ƙasashen biyu ta yi tsami.
Aljazeera ta rahoto cewa a farkon 2022, Mali ta kori jakadan Faransa, lamarin da ya sa Faransa ta janye sojojinta da dakarun Takuba daga ƙasar.
5. Shugaban Senegal ya kori sojojin Faransa
Kwanan nan shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya bada umarnin rufe sansanonin sojin Faransa da ke kasar, inda ya danganta matakin da ‘yancin Senegal.
Da yake jawabi gabanin cika shekaru 80 da kisan kiyashin da turawan mulkin mallaka suka yi wa sojojin Senegal a 1944, Faye ya ce Shugaba Emmanuel Macron ya amince Faransa na da hannu a danyen aikin.
Faye ya ce zaman Faransa ya saba wa ‘yancin kan Senegal, yana mai jaddada cewa kasa mai cikakken iko ba za ta dauki nauyin sojojin kasashen waje ba, rahoton France 24.
6. Gwamnatin Burkina Faso ta kori sojin Faransa
Bayan da sojojin Faransa 4,500 na Operation Barkhane suka fice daga Mali a watan Agustan 2022, ƴan uwansu sun bar Burkina Faso a watan Fabrairun 2023.
Sojoji 400 na rundunar Operation Sabre da aka girke a 2009 domin yakar kungiyoyin ƴan tada ƙayar baya kamar al-Qaeda, sun fice daga Burkina Faso cikin lalama.
Hakan ya biyo bayan umarnin da gwamnatin sojin Burkina Faso ta bayar kuma ta ba sojojin na Faransa wa'adin makonni huɗu su tattara su bar ƙasar, Reuters ta kawo.
DHQ ta musanta kafa sansanin sojin Faransa
Kun ji cewa hedkwatar tsaro ta ƙasa watau DHQ ta musanta jita-jitar da ke yawo cewa sojojin ƙasar Faransa za su kafa sansani a Najeriya.
Kakakin DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa labarin tsagwaron karya ce da wasu suka kirkira da wata manufa ta daban.
Asali: Legit.ng