Juyin mulkin Mali: Fuskokin zakakuran sojojin da suka ture gwamnati

Juyin mulkin Mali: Fuskokin zakakuran sojojin da suka ture gwamnati

- A ranar Talata, 18 ga watan Augustan 2020 aka yi wa shugaban kasa Boubacar Keita juyin mulki

- Kanal Malick Diaw, Sadio Camara da Laftanal kanal Mama Seku Lelenta suka shirya juyin mulkin

- Kanal Diaw shine shugaban ma'aikatan kuma na uku a yankin Kati

A ranar Talata, 18 ga watan Augustan 2020, an yi wa shugaban kasar Mali, Boubacar Keita, juyin mulki.

Legit.ng ta gano cewa, wadanda suka shirya juyin mulkin sun hada da Kanal Malick Diaw, Sadio Camara da Laftanal Kanal Mama Seku Lelenta.

Kamar yadda PM News ta bayyana, Camara shine tsohon daraktan rundunar Prytaneum a Kati, wanda bai dade da dawowa daga horarwa ba a kasar Rasha.

Wasu kafofin yada labarai sun yi ikirarin cewa, Diaw na da shekaru 25 a duniya, amma Legit.ng bata san sahihancin zancen ba.

Sojan mai mukamin Kanal shine shugaban ma'aikata kuma na uku a yankin Kati.

Wadanda suka shirya juyin mulkin sun tsinkayi birnin Bamako a ranar Talata inda suka dinga kama manyan jami'an gwamnatin kasar Mali.

Baya ga shugaban kasa Keita da firayim minista Boubou Cisse, sun kama jami'ai da yawa da suka hada da shugaban ma'aikatan tsaro kuma daraktan kudi, Abdoulaye Daffe, ministan tattalin arziki da kudi da kuma ministan harkokin waje.

Juyin mulkin Mali: Fuskokin zakakuran sojojin da suka ture gwamnati
Juyin mulkin Mali: Fuskokin zakakuran sojojin da suka ture gwamnati. Hoto daga PM News
Asali: UGC

Juyin mulkin Mali: Fuskokin zakakuran sojojin da suka ture gwamnati
Juyin mulkin Mali: Fuskokin zakakuran sojojin da suka ture gwamnati. Hoto daga PM News
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon matar da ta haifa 'ya'ya 44 a yayin da ta cika shekaru 40

Juyin mulkin Mali: Fuskokin zakakuran sojojin da suka ture gwamnati
Juyin mulkin Mali: Fuskokin zakakuran sojojin da suka ture gwamnati. Hoto daga PM News
Asali: UGC

Shugaban majalisar dattawan kasar, Moussa Timbine, yana hannun mashiryan juyin mulki.

Idan za mu tuna, shugaban kasar ya hanzarta yin murabus bayan sa'o'i kadan da kama shi, lamarin da ya kawo matukar farin ciki a kasar Mali baki daya.

Kafin nan, 'yan kasar Mali suna ta mika bukatar murabus din shugaban kasar, amma bayan saukarsa, sun kasa iya boye murnarsu tare da godiyarsu ga mashirya juyin mulkin.

Amma kuma, a ranar Talata, kungiyar hadin kan kasashen Afrika na yamma, sun kushe abinda ya faru a kasar Mali tare da daukar alkawarin ladabtarwa wanda ya hada da tara.

A wata takarda da ECOWAS ta aike musu, ta ce dukkan kasashen Afrika ta yamma za su rufe iyakokin da ke tsakaninsu da Mali na kasa da na sama kuma za ta ci tararsu.

Kungiyar kasashen 15 wanda ya hada da Mali, ta kara da cewa za ta dakatar da kasar daga cikin masu yanke hukuncinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng