Elon Musk Ya Goge Raini, Ya Tabbata Mai Kudin Duniya da Dukiyarsa Ta Kai $447bn

Elon Musk Ya Goge Raini, Ya Tabbata Mai Kudin Duniya da Dukiyarsa Ta Kai $447bn

  • Idan aka tambaye ka wanene mutumin da ya fi kowa yawan dukiya a yanzu a duniya, amsar ita ce Elon Musk
  • Musk mai shekara 53 ya yi wa Jeff Bezos nisa a jerin masu arziki, dukiyarsa ta na neman kai Dala biliyan 500 a yau
  • Attajirin yana cigaba da ganin karin arziki tun da gwaninsa watau Donald Trump ya yi nasara a zaben Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

America - Shugaban kamfanin Tesla mai kera motocin da ke amfani da lantarki, Elon Musk, shi ne kan gaba a masu kudin duniya.

Elon Musk wanda haifaffen kasar Afrika ta Kudu ne da ke zama a Amurka ya zarce kowa, ya mallaki abin da ya haura dala biliyan 400.

Elon Musk
Elon Musk ya ba Jeff Bezos rata mai yawa a sahun attajirai a duniya Hoto; @Yegwave/@JDCocchiarella
Asali: Twitter

Elon Musk ya dame Jeff Bezos a kudi

Bayanan da aka samu daga Bloomberg Billionaires Index sun tabbatar da cewa Elon Musk ya mallaki kudin da ba a taba gani ba.

Kara karanta wannan

'Ba ku da hankali ne': Akpabio ga masu fada da Ministan Tinubu, ya jero dalilansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A karshen makon nan dukiyar attajirin ta kai $447bn, hakan ya na nufin ya sha gaban mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos da $190bn.

Dukiyar Musk wanda ya yi wa Donald Trump kamfe har ya samu mukami a gwamnatin Amurka ta na cigaba da habaka a yanzu.

Musk yana ganin riba a kasuwancinsa

Jaridar Wall Street Journal ta ce hannun jarin kamfanin Tesla ya tashi a Disamban nan.

Rahotanni sun ce attajirin wanda yanzu shi ya mallaki kamfanin X shi ne mutumin farko da aka taba ji ya ba Dala biliyan 400 a baya.

Idan aka yi lissafi a kudin Najeriya, dukiyar Musk ta kai Naira tiriliyan 690 kenan. Fox News ta ce zai iya sayen kamfanin X sau 10 a yau.

A ranar Juma’a Fortune India ta rahoto cewa abin da Musk ya mallaka ya karu da fiye da $100bn a ‘yan kwanakin nan na karshen 2024.

Kara karanta wannan

'Ku biya haraji': Fitaccen mawakin Arewa ya saki bidiyon da ya jawo masa zagi

Ana alakanta karin dukiyar Musk da nasarar da Donald Trump ya samu a kan Kamala Haris da jam’iyya mai mulki a zaben Amurka.

Elon Musk ya shiga siyasar Amurka

Ana da labarin yadda Elon Musk ya yi magana kan nasarar Donald Trump, yake cewa hakan ya nuna mutanen kasar Amurka na son canji.

Trump dai ya doke abokiyar hamayyarsa Kamala Harris a zaben shugaban ƙasan Amurka da taimakon irinsu Musk a dandalin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng