Kifar da Gwamnatin Assad a Siriya Ya Jawo Saukar Farashin Man Fetur

Kifar da Gwamnatin Assad a Siriya Ya Jawo Saukar Farashin Man Fetur

  • Farashin gangar danyen mai na Brent ya sauka zuwa $72.06, yayin da na WTI ya dawo $68.23 bayan kifewar gwamnatin Bashar al-Assad
  • Duk da Siriya ba babbar kasa ce mai arzikin mai ba, matsayinta a duniya yana da tasiri sosai kan kasuwannin man fetur a duniya
  • Rahotanni sun nuna cewa cigaban tattalin arziki na duniya da tattalin arzikin Amurka da China sun rage tasirin saukin farashin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Syria - Farashin man fetur a duniya ya yi kasa kadan, inda ya kai $72 a kan kowace ganga a ranar Talata, bayan kifewar gwamnatin Shugaban Siriya Bashar al-Assad.

Rahotanni sun nuna cewa sauyin shugabanci a Siriya ya rage damuwar da ake da ita kan yiwuwar rikici a yankin, wanda ke da tasiri kan kasuwannin man fetur na duniya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ɓarin wuta a cikin gari, sun yi garkuwa da hadimin tsohon gwamna

Fetur
Farashin danyen mai ya sauka a Duniya. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Rahoton Reuters ya nuna cewa cigaban tattalin arziki Amurka da China sun taimaka wajen rage tasirin saukin farashin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farashin mai ya sauka bayan kifewar da Assad

Bayan kifewar gwamnatin Assad ranar Lahadi 8 ga Disamba, farashin man fetur ya fadi daga karin sama da 1% da aka samu a ranar Litinin.

Farashin gangar mai na Brent ya sauka da 0.11% zuwa $72.06, yayin da na WTI ya ragu da 0.20% zuwa $68.23.

Tasirin kasar Siriya kan harkokin man fetur ya samo asali daga matsayinta a siyasar duniya da kuma kawancenta da kasashen Rasha da Iran.

Alakar saukar farshin mai a kasuwa da Siriya

Kifewar gwamnatin Assad, wadda ta kwashe shekaru 14 a mulki, ya sanya 'yan tawayen Siriya fara sake gina bangarori masu muhimmanci, ciki har da bangaren man fetur.

An fara samun ci gaba a harkokin fitar da mai daga kasar a ranar Talata, lamarin da ya rage damuwa kan tsadar mai a duniya.

Kara karanta wannan

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya fadi abin da zai faru da tattalin Najeriya kwanan nan

Leadership ta wallafa cewa OPEC ta tsawaita damar fitar da man Najeriya na ganga miliyan 1.5 a kowace rana har zuwa 2026, wanda ke da tasiri wajen tsayar da farashin man a duniya.

Kwastam ta rage farashin mai a Najeriya

A wani rahoton kun ji cewa hukumar kwastam ta kama man fetur mai tarin yawa da aka nufi fita da shi daga Najeriya da barauniyar hanya.

An ruwaito cewa kakakin hukumar ya bayyana cewa za su sayar da man fetur din ga yan Najeriya a farashi mai rahusa a jihar Adamawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng