Abba Ya Ziyarci Daliban Kano a Indiya, zai Cigaba da Daukar Nauyin Karatun Talakawa
- Gwamna jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yabawa ƙwazon ɗaliban da gwamnatinsa ta tura karatu zuwa kasar Indiya
- Alamu sun nuna cewa ziyarar gwamnan ta bai wa ɗaliban damar bayyana ƙalubale da nasarorin da suka samu
- Gwamnan ya ce za a tabbatar da cigaba da shirin tallafin karatu har ƙarshen wa’adin gwamnatinsa ta farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
India - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a jami'ar Sharjah ta kasar India.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Abba Kabir ya yi ziyarar ne domin duba halin da daliban ke ciki bayan shafe lokaci a kasar.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a Facebook Abba ya nuna farin ciki bisa kokarin ɗaliban.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da bai wa ilimi muhimmanci, yana mai bayyana cewa tallafa wa matasa wajen neman ilimi wani mataki ne mai muhimmanci domin ci gaban Kano.
Tallafin karatu ya yi amfani inji Abba
Gwamnan ya bayyana gamsuwa da yadda ɗaliban jihar suka yi ƙoƙari a karatunsu, yana mai cewa nasarorin suna tabbatar da cewa ba a yi asarar kudin da aka kashe ba.
Abba Kabir ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da saka hannun jari a ilimi domin haɓaka basirar matasa a jihar Kano.
Shirin sake tura daliban Kano jami'o'i
Gwamnan ya bayyana cewa ziyarar da ya kai ta ba shi damar duba matakan da suka dace wajen shirin tura ɗalibai na gaba cikin shirin tallafin karatu na 100:1.
Abba Kabir Yusuf ya kuma tabbatar da cewa za cigaba da tura dalibai karatu ne zuwa jami'oin gida Najeriya da ketare.
Abba zai cigaba da ziyarar jami'oi a Indiya
A wani sako na daban, Sanusi Bature ya wallafa a Facebook cewa gwamnan zai ziyarci wasu jamio'i da suka hada da Symbiosis, Kalinga da Shuwanin.
Ziyarar ta kasance wata dama ta karfafa ɗaliban kan muhimmancin ƙwazo da sadaukarwa, domin ganin sun kasance jakadu masu alfahari da jihar Kano.
Za a tura daliban Kano jami'o'i
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara kara shirin tura ƴaƴan talakawa karatu jami'o'i.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamiti mai dauke da mutane 18 da zai tantance daliban da za a zaba kafin a tura su karatun.
Asali: Legit.ng