Muhimman Abubuwa 10 da Tinubu Ya Fada yayin Jawabinsa a Kasar Afrika ta Kudu

Muhimman Abubuwa 10 da Tinubu Ya Fada yayin Jawabinsa a Kasar Afrika ta Kudu

A yau Talata, 3 ga watan Disamba shugaba Bola Tinubu ya yi jawabi yayin taron Najeriya da Afrika ta Kudu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

South Africa - Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi yayin taron Najeriya da Afrika ta Kudu na 11.

Bola Tinubu ya mayar da hankali kan wasu abubuwa masu muhimmanci da suka nuna alakar Najeriya da Afrika ta Kudu.

Tinubu
Jawabin Tinubu a Afrika ta Kudu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku muhimman abubuwa 10 da daga cikkin jawabin shugaban kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Dangantaka mai tsawon tarihi

Shugaba Tinubu ya yaba da alaƙa mai kyau da ke tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu, wanda aka gina bisa haɗin kai a lokacin yaki da wariyar launin fata.

Kara karanta wannan

Sultan da shugaban CAN sun ajiye bambancin addini, sun mika bukata 1 ga Tinubu

2. Jagorantar Afrika

Rahoton the Nation ya nuna cewa ya jaddada nauyin da ke kan ƙasashen biyu na jagorantar Afirka wajen cimma ’yanci, daidaito da kyakkyawan shugabanci.

3. Lura da lamuran matasa

Tinubu ya jaddada muhimmancin ba da dama da ake ga matasa a ƙasashen biyu, yana bayyana matasa a matsayin babbar madogarar Afirka wajen ci gaba.

4. Haɗin kan tattalin arziki

Shugaban ya yi kira ga Najeriya da Afirka ta Kudu su jawo ci gaban tattalin arziki a Afirka tare da ƙarfafa dangantaka a ƙarƙashin Yarjejeniyar Cinikayya ta Afirka (AfCFTA).

5. Kira ga cigaba da aiki tare

Bola Tinubu ya yi kira ga ƙasashen biyu su mai da hankali kan aiwatar da yarjejeniyoyi da fahimtar juna (MoUs) da aka rattaba hannu a kai tsawon shekaru.

6. Kyakkyawar alakar kasuwanci

Tinubu ya yaba da nasarar kamfanonin Afirka ta Kudu kamar MTN da Multichoice a Najeriya, da na Najeriya kamar Dangote da bankin Access a Afirka ta Kudu, amma ya nuna bukatar magance matsalolin da ake samu.

Kara karanta wannan

Afrika ta Kudu: Ramaphosa ya fadi ta fuskar da ya ke fatan karfafa alaka da Najeriya

7. Haɗin kai tsakanin matasa

Tinubu ya yi kira ga ƙarin haɗin kai tsakanin matasan Najeriya da Afirka ta Kudu, yana ƙarfafa haɗin gwiwa da zai samar da ci gaba.

8. Yaki da hakar ma'adinai ba bisa ka’ida ba

Tinubu ya ba da shawarar ƙirƙirar ƙungiyar ƙasashen Afirka don yaki da hakar ma'adinai ba bisa ka’ida ba, yana mai bayyana lamarin a matsayin barazana ga zaman lafiyar tattalin arziki, muhalli da shugabanci a nahiyar.

9. Zamowa abin misali a Afrika

The Guardian ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana haɗin kan Najeriya da Afirka ta Kudu a matsayin abin koyi ga sauran kasahe a faɗin nahiyar.

10. Fitar da Afrika a kunya

A karshe, Tinubu ya ƙalubalanci ƙasashen biyu su yi aiki tare domin canza yadda duniya ke yi wa Afrika kallon raini.

Tinubu ya rarrashi yan Najeriya

Kara karanta wannan

Tinubu ya saurari kukan jama'a kan ƙudirin haraji, ya ba da sabon umarni

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga yan Najeriya da su kara hakuri kan halin wahalar rayuwa da suke ciki.

Haka zalika gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce tabbas ana fama da wahalar rayuwa amma sun jajirce wajen kawo karshen matsalar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng