Lokaci Ya Yi: Mutumin da Ya Fi Kowa Tsufa a Duniya Ya Mutu Yana da Shekara 112

Lokaci Ya Yi: Mutumin da Ya Fi Kowa Tsufa a Duniya Ya Mutu Yana da Shekara 112

United Kingdom - Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya, dan asalin ƙasar Birtaniya John Tinniswood, ya mutu yana da shekara 112.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

An haifi Tinniswood a Liverpool a ranar 26 ga Agusta, 1912, kuma ya mutu ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba, 2024.

John Tinniswood.
Mutum mafi tsufa a duniya ɗan salin ƙasar Birtaniyaya mutu yana da shekara 112 Hoto: @GWR
Asali: Twitter

Kundin gwaninta 'Guinness World Records' mai tattara bayanan tarihi a duniya ya tabbatar da mutuwar mutumin a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X ranar Talata.

Ya zama mutum mafi tsufa a duniya a watan Afrilu bayan mutuwar Juan Vicente Perez dan kasar Venezuela mai shekaru 114.

"Yana kewaye da ƙida da ƙauna a ranarsa ta ƙarshe duniya," in ji danginsa a cikin wata sanarwa da suka fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyalan marigayin sun godewa dukkan waɗanda suka nuna kulawarsu a kan John Tinniswood a lokacin rayuwarsa.

Karin bayani na nan tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262