Bayan Umarnin Kama Netanyahu, Isra'ila na Shirin Tsagaita Wuta a Lebanon
- Ana shirin tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da yan Hisbullah a kasar Lebanon bayan ɗaukar lokaci ana kai munanan hare hare
- Wakilin kasar Amurka, Amos Hochstein ne ke jagorantar tattaunawa wajen kawo karshen yakin na wani lokaci kafin a kawo karshensa baki daya
- Hakan na zuwa ne bayan kotun hukunta masu manyan laifuffuka ta ICC ta bayar da umarni a kama Benjamin Netanyahu a makon da ya wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lebanon - Kokarin da Amurka ta fara na kawo karshen rikicin Isra'ila da Hisbullah ya fara haifar da ɗa mai ido.
Kasar Isra'ila ta nuna alamar amincewa da shirin tsagaita wuta a Lebanon da Amurka ke jagoranta.
Rahotan CNN ya nuna cewa har yanzu ana kan tattaunawa domin cimma matsaya a tsakanin kasashen.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Isra'ila za ta tsagaita wuta a kasar Lebanon
Kasar Isra'ila ta nuna amincewa da tsagaita wuta a kasar Lebanon a kan yakin da ta ke da ƙungiyar Hisbullah.
A yanzu haka tattaunawa ta yi nisa kuma ana jiran kasar Isra'ila ta amince da shirin a hukumance.
Wakilin Amurka mai shiga tsakani, Amos Hochstein ya ce idan Isra'ila ta yi jinkirin amincewa da shirin zai zare hannunsa a ciki.
Lebanon: Za a tsagaita wutar kwanaki 60
Dan kasar Amurka mai shiga tsakani, Amos Hochstein ya bayyana cewa za a tsagaita wutar ne a tsawon kwanaki 60.
Rahotan Reuters ya nuna cewa za a tsagaita wutar ne a kwanakin domin lalubo hanyar kawo karshen rikicin baki daya.
Yaushe za a tsagaita wuta a Lebanon?
A makon da ya wuce Amos Hochstein ya gana da wakilan Hisbullah a Lebanon kafin ya wuce kasar Isra'ila.
Sai dai Isra'ila ta nuna shakku kan wasu abubuwa da Lebanon ta ambata a cikin sharudan tsagaita wutar wanda a yau Litinin ake sa ran Isra'ila za ta yi matsaya domin kawo karshen yakin.
Kasar Isra'ila ta kai hari a Iran
A wani rahoton, mun ruwaito muku cewa Isra'ila ta kai harin ramuwar gayya kan ƙasar Iran a wani yunƙuri na ƙara takalar faɗa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ƙasar Iran ta tabbatar da kai hare-haren a kan sansanonin soji da ke wasu larduna guda uku na ƙasar ciki har da birnin Tehran.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng