Kotun ICC Ta ba da Sammacin Cafke Netanyahu da Wasu Kwamandojin Hamas

Kotun ICC Ta ba da Sammacin Cafke Netanyahu da Wasu Kwamandojin Hamas

  • Kotun manyan laifuffuka ta ICC ta ba da sammacin kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan yake-yake
  • Kotun ta kuma ba da takardar sammacin domin cafke tsohon ministan tsaron Isra'ila da kuma wasu kwamandojin kungiyar Hamas
  • Hakan ya biyo bayan cigaba da zubar da jini da ake yi a Gabas ta Tsakiya tsakanin Isra'ila da Hamas tsawon lokaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Isra'ila - Yayin da ake cigaba da zubar da jini a Gabas ta Tsakiya, kotun manyan laifuffuka (ICC) za ta dakile matsalar.

Kotun ta bayar da sammacin cafke Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da tsohon ministan tsaron kasar.

Kotun ICC za ta cafke Netanyahu da wasu a kungiyar Hamas
Kotun ICC ta gaji da rikicin Isra'ila da Hamas, ta tura takardar sammaci. Hoto: Kent Nishimura.
Asali: Getty Images

Kotun ICC ta ba da sammaci ga Netanyahu

Rahoton CNN ya ce bayan sammaci ga Netanyahu, an kuma ba da takardar ga wasu kwamandojin kungiyar Hamas.

Kara karanta wannan

Abba Hikima ya jagoranci maka Wike a kotu kan wulakanta yan Arewa a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alƙalan kotun ICC sun bayyana cewa sun yi watsi da yunƙurin Isra'ila na ƙalubalantar ikon da kotun ke da shi kan sauraron shari'ar.

Har ila yau, an bayar da sammacin kama Mohammed Deif, duk da cewa sojojin Isra'ila sun ce sun kashe shi a wani hari a Gaza a watan Yulin 2024, cewar rahoton Newsweek.

Musabbabin shigar da Netanyawu kara a ICC

Hakan ya biyo bayan gabatar da kara da Karim Khan ya yi a kotun ICC inda ya bukaci hukunta Netanyahu da Gallant da Deif kan laifuffukan yaki.

Khan ya shigar da korafi ne a watan Mayun 2024 kan Netanyahu da wasu kwamandojin Hamas duk da cewa an kashe guda biyu daga cikin sannan Isra'ila ta ce ta hallaka Deif.

Yan Najeriya sun caccake Isra'ila kan Iran

A baya, kun ji cewa asu yan Najeriya da dama sun caccaki kasar Isra'ila da ke neman hada kasar fada da Iran da ke Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

An miƙawa gwamnatin Tinubu buƙatar daukar mataki kan haihuwa barkatai

akan ya biyo bayan zargin da Isra'ila ta yi cewa Iran na da hannu a neman ruguza Najeriya da rashin tsaro.

Sai dai yan kasar sun kushe salon Isra'ila na neman hada kasar fada da Iran kan wasu zarge-zarge da ba su da tushe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.