Biden Ya Taro Rigima da Amurka Ta Taimaki Ukraine, Putin Zai Halatta Amfani da Nukiliya
- Amurka ta takalo tsokanar Rasha bayan an tabbatar da ta ba kasar Ukraine makamai masu nisan zango
- Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya gaggauta sassauta dokar amfani da makaminta na kare dangi
- Rasha ta gargadi Amurka da Faransa kan yin katsalandan a yakin da ta ke gwambazawa tsakaninta da Ukraine
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Rasha - Yakin Rasha da Ukraine na shirin daukar sabon salo bayan Amurka ta ba Ukraine din makamai masu dogon zango.
Haka kuma kasar Rasha ta zargi Amurka da ba Ukraine wasu makamai da aka kai mata hari har cikin kasar da su.
Kafar Reuters ta ruwaito cewa yanzu haka shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya dauki matakin da ka iya dagula yakin da ake gwabzawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rasha ta sassauta dokar amfani da makamin nukiliya
Time Magazine ta ruwaito cewa cewa shugaban Rasha, Vladimir Putin ya sassauta da dokar amfani da makamin nukiliya a kasar.
Wannan na zuwa ne bayan zargin Amurka da shiga yakin da ta ke yi da kasar Ukraine ta hanyar ba ta makaman kai hari cikin Rasha.
Dokar Rasha ta bayyana cewa za ta iya amfani da makamin nukiliya, wanda ake kira da makamin kare dangi idan ana yi mata barazana a matsayin kasa
Ukraine: Rasha ta shiga takun saka da Amurka
A baya, kasar Rasha ta sha gargadin kasashen Amurka da Faransa kan ba Ukraine makamai domin cigaba da gwabza yaki da ita.
Vladimir Putin ya nanata cewa duk lokacin da hakan ta faru, kasarsa za ta dauka cewa NATO ta shiga yakin da ta ke yi da Ukraine kai tsaye.
Jiragen yaki sun kai hari a Rasha
A baya mun ruwaito cewa jiragen yaki marasa matuka sun farmaki fadar shugaban Rasha, Vladimir Putin yayin da yakin da ya ke yi da Ukraine ke kara karamari.
Bayan kai harin ne Rasha ta gaggauta nuna yatsa ga Ukraine da cewa ita ce ta kai harin, lamarin da Ukraine ta musa tare da cewa ta fi mayar da hankali kan kwato yankunanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng