Shugaban Iran na Kwance Rai a Hannun Allah? Bayanai Sun Fito

Shugaban Iran na Kwance Rai a Hannun Allah? Bayanai Sun Fito

  • Hukumomin kasar Iran sun yi martani kan labarin da ake yadawa na cewa shugaba Ayatullah Ali Khamenei na kwance
  • Kafofin sadarwan kasar Iran sun ƙaryata labarin inda suka nuna shugaban yana ayyuka a ofishinsa a ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamba
  • An nuno hoton shugaba Ayatullah Ali Khamenei yana tattaunawa da Ambasadan Iran da ke kasar Lebanon, Mojtaba Amani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Kasar Iran ta yi bayani kan labarin da aka rika yadawa cewa shugaban juyin juya hali, Ayatullah Ali Khamenei ba shi da lafiya.

Rahotanni sun nuna cewa wasu kafafen yada labarai ne a ƙasashen Turai suka yada labarin da Iran ta ce ba shi da tushe.

Kasar Iran
Iran ta yi bayani kan lafiyar shugabanta. Hoto: @Khamenei_fa
Asali: UGC

Legit ta gano bayanan da Iran ta yi a kan lafiyar Ayatullah Ali Khamenei ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafin shugaban na X.

Kara karanta wannan

Paraguay: Rashin lafiya ya kama shugaban ƙasa ana tsaka da taron da Tinubu ya Tafi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar rashin lafiyar Khamenei

Tun a makon da ya wuce wasu kafafen yada labarai a kasashen Turai suka rika yada labarin cewa Ayatullah Ali Khamenei ba shi da lafiya.

Rahoton Times of India ya nuna cewa kafafen yada labaran sun yi ikirarin cewa shugaban yana kwance rai a hannun Allah.

Shugaban Iran yana lafiya kalau

A wani martani da ta yi, kasar Iran ta ƙaryata zancen cewa shugaba Ayatullah Ali Khamenei ba shi da lafiya.

A karkashin haka, Iran ta wallafa hoton Ayatullah Ali Khamenei da wani jami'in gwamnati suna wata tattaunawa.

"Shugaban Ayatullah Ali Khamenei ya hadu tare da tattaunawa da ambasadan Iran a Lebanon, Mojtaba Amani a yammacin yau.
Tattaunawar da Ayatullah Ali Khamenei ya yi da Mojtaba Amani na cikin jerin ayyukan yau da kullum da yake yi a ofis."

- Gwamnatin kasar Iran

Mojtaba Amani na cikin waɗanda suka samu rauni a wani harin bom da aka kai Lebanon da ya kashe mutane kimanin 39 a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Hattara yan TikTok: An daure matashi a gidan kaso kan zagin shugaban kasa

Iran ta kai hari a kasar Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa rahotanni na nuni da cewa an kai zafafan hare hare a Tel Aviv, babban birnin kasar Isra'ila.

An ruwaito cewa kasar Iran ce ta dauki nauyin kai hare haren kuma ta bayyana dalilan da suka sanya ta daukar matakin a kan Isra'ila.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng