Paraguay: Rashin Lafiya Ya Kama Shugaban Kasa Ana Tsaka da Taron da Tinubu Ya Tafi
- Rahotanni da suka fito daga Brazil na nuni da cewa shugaban kasar Paraguay ya kamu da rashin lafiya ana tsaka da taron G20
- Gwamnatin Paraguay ta tabbatar da an mika Santiago Pena zuwa asibiti domin duba lafiyarsa da ba shi kulawa ta musamman
- Bayan yi wa shugaba Santiago Pena gwaje gwaje, hukumomi sun Paraguay sun bayyana halin da shugaban kasar ya ke ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Brazil - Hukumomin kasar Paraguay sun tabbatar da cewa shugaban kasarsu, Santiago Pena ya kamu da rashin lafiya a taron kasashen G20.
Ana gudanar da taron ƙasashen G20 a kasar Brazil ne kuma shugaba Bola Tinubu na Najeriya ma ya samu halarta.
Rahoton Reuters ya tabbatar da cewa a yanzu haka shugaban kasa Santiago Pena na cikin yanayi mai kyau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kasa ya fara rashin lafiya a taro
A yammacin ranar Litinin shugaban kasar Paraguay, Santiago Pena ya kamu da rashin lafiya ana tsaka da taron kasashen G20 a Brazil.
Times of India ta wallafa cewa an garzaya da shugaban kasar mai shekaru 46 asibitin Samaritano a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil.
"Muna sanar da ku cewa an mika shugaban kasa, Santiago Pena asibiti bisa rashin lafiya ana taron kasashen G20.
A yanzu haka shugaban kasar yana karɓar kulawa a asibitin Samaritano na birnin Rio de Janeiro."
- Gwamnatin Paraguay
Alliana ya yi magana da shugaban Paraguay
Bayan yi masa gwaje gwaje, matar shugaban kasar, Leticia Ocampos ta ce a yanzu haka Santiago na cikin yana yi mai kyau.
Haka zalika mataimakin shugaban kasar Paraguay, Pedro Alliana ya ce ya yi wayar tarho da shugaban kasar kuma matsalar da ta same shi karama ce.
Kafin rashin lafiyar, shugaba Santiago Pena ya ce za su mayar da hankali wajen yaki da dumamar yanayi a duniya yayin da yake zaune kusa da Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya shiga hadakar yaki da yunwa
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya Najeriya cikin sabuwar kungiyar kawancen kasashen duniya da aka kafa a Brazil.
Shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya kirkiro kungiyar da nufin yakar yunwa da talauci a kasashen duniya baki daya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng