'Babu Ruwanmu a Fadanku': An Soki Isra'ila da Ta Zargi Wata Ƙasa da Neman Ruguza Najeriya
- Wasu yan Najeriya da dama sun caccaki kasar Isra'ila da ke neman hada kasar fada da Iran da ke Gabas ta Tsakiya
- Hakan ya biyo bayan zargin da Isra'ila ta yi cewa Iran na da hannu a neman ruguza Najeriya da rashin tsaro
- Sai dai yan kasar sun kushe salon Isra'ila na neman hada kasar fada da Iran kan wasu zarge-zarge da ba su da tushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yan Najeriya da dama sun tofa albarkacin bakinsu game da zargin Isra'ila kan kasar Iran.
Yan kasar sun gargadi Isra'ila ta guji kawo rigimar da suke yi tsakaninsu a Gabas ta Tsakiya zuwa Najeriya.
Isra'ila ta zargi Iran da neman tarwatsa Najeriya
Tribune ta ruwaito cewa jakadan Isra'ila a Najeriya, Michael Freeman ya zargi Iran da neman kawo tarnaki a zaman lafiyar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Freeman ya fadi haka ne a Abuja yayin bikin cika shekara daya da Hamas ta yi kisan gilla kan yan Isra'ila.
Freeman ya nuna damuwa kan yadda ake fama da matsalar tsaro musamman a Najeriya inda ya zargi Iran da hannu a ciki, cewar Thisday.
Sai dai wannan zargi ya jawo ka-ce-na-ce a Najeriya musamman a kafofin sadarwa ta zamani.
Martanin wasu yan Najeriya kan zargin Isra'ila
@Jonehmk:
"Malam, Najeriya ba za ta yadda da zargin da kake yi ba kan Iran, ka da ka dauko fadanku da Iran ka jawo matsala tsakanin Abuja da Tehran."
@MohWorldent:
"Sun dage sai sun jawo rigima tsakanin Najeriya da kowace kasa karfi da yaji."
@SavannaConnect:
"Wannan babban zargi ne, idan har gaskiya ne zai iya kawo cikas ga zaman lafiyar Najeriya, ya kamata Najeriya ta yi bincike domin kare martabarta."
@HEATHEN_STONER:
"Ku duba yadda yan Najeriya ke amincewa da karyar Isra'ila, ina zargin Isra'ila na da hannu a lalata Najeriya musamman a yakin basasa da suka goyi bayan kasar."
@demobanty:
"Wannan ba wani abu ba ne, babu wanda zai amince da wani ko abin da ke da alaƙa da Isra'ila."
Isra'ila ta kai wasu hare-hare kasar Iran
A baya, kun ji cewa Isra'ila ta kai harin ramuwar gayya kan ƙasar Iran a wani yunƙuri na ƙara takalar faɗa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Ƙasar Iran ta tabbatar da kai hare-haren a kan sansanonin soji da ke wasu larduna guda uku na ƙasar ciki har da birnin Tehran.
Asali: Legit.ng