Bidiyon Lokacin da Tinubu Ya Isa Birnin Riyadh, Zai Halarci manyan Tarurruka 2

Bidiyon Lokacin da Tinubu Ya Isa Birnin Riyadh, Zai Halarci manyan Tarurruka 2

  • Shugaba Bola Tinubu ya isa Saudia domin halartar taron da zai kara hadin kai tsakanin kasashen Larabawa da Musulunci
  • Taron, wanda za a gudanar a kwanaki biyu, zai tattauna kan kasuwanci, yaki da ta'addanci, da ci gaban ababen more rayuwa
  • Ana tunanin Tinubu yana shirin bunkasa kasuwanci, zuba jari, da habaka tattalin arzikin Najeriya ta hanyar wannan taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Saudiya - Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiya a ranar Lahadi, 10 ga watan Nuwambar 2024.

An ce Tinubu ya je Saudiya domin halartar manyan tarurruka guda biyu, wadanda za su mai da hankali kan ƙarfafa dangantakarkasashen Larabawa da Musulunci.

Kara karanta wannan

Jigo ya tsallake Kwankwaso, Atiku, ya fadi wanda zai karbi mulki hannun Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiya
Shugaba Tinubu ya isa Saudiya domin halartar taron kasashen Larabawa da Musulunci. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Saudiya: Tinubu ya isa birnin Riyadh

Channels TV ta rahoto cewa tarurrukan za su gudana ne daga ranar 10 zuwa 11 ga Nuwamba, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce za a tattauna batutuwa masu muhimmanci kamar kasuwanci, yaki da ta'addanci, gami da haɗin gwiwar gina titunan jirgin kasa.

An ce Tinubu, wanda kuma shi ne Shugaban ECOWAS, zai yi amfani da taron wajen inganta kasuwanci da zuba jari tsakanin Najeriya da kasashen Larabawa.

Tasirin zuwan Tinubu taron Saudiya

Ana sa ran ziyarar tasa za ta jawo zuba jari daga ƙasashen waje domin inganta tattalin arzikin Najeriya, musamman a fannonin masana'antu.

Burin Tinubu na jawo masu zuwa jari zuwa kasar ya ta'allaka ga samar da ayyukan yi, bunkasa tattali da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa wajen bunƙasa gine-gine.

Ana sa ran cewa halartar Shugaba Tinubu zai amfanar da ci gaban tattalin arzikin Najeriya da matsayinta na ginshikin kasuwanci a kasuwannin duniya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai lula ƙasar waje, zai halarci muhimmin taro da ya shafi Musulunci

Kalli bidiyon lokacin da Tinubu ya isa Saudiya a kasa:

Tinubu zai shilla zuwa kasar Saudiya

Tun da fari, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu zai kama hanyar zuwa Saudiyya gobe Lahadi domin halartar taron ƙasashen Larabawa da Musulunci.

Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya ce Tinubu zai yi magana kan rikicin Isra'ila da Falasɗinu tare da jaddada bukatar tsagaita wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.