A Karshe, Kamala Harris Ta Kira Zaɓabɓen Shugaban Ƙasar Amurka Ta Wayar Tarho
- Ƴar takarar jam'iyyar Democrat, Kamala Harris ta kira zababben shugaban kasar Amurka, Donald Trump ta wayar tarho bayan ta sha kaye
- Mataimakiyar shugaban Amurka ta taya Trump murnar lashe zaɓe tare da tabbatar da cewa za ta taimaka a miƙa mulki cikin lumana
- Donald Trump dai ya samu nasarar doke Kamala Harris, inda zai zama shugaban Amurka na 47 a tarihi idan aka rantsar da shi a 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
United States - Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris ta kira Donald Trump a ranar Laraba ta wayar tarho domin taya shi murnar lashe zaben shugaban kasa na 2024.
Ɗaya daga cikin hadiman Kamala Harria ne ya bayyana haka bayan kammala zaben wanda aka fafata tsakaninta da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.
Kamala Harris ta taya Trump murna
Ƴar takarar jam'iyyar Democrat, Harris da Trump sun tattauna kan mahimmancin mika mulki cikin lumana da zama shugaban kasa ga dukkan Amurkawa,
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta kuma taya zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Amurka murnar wannan nasara da ya samu a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta da manhajar X.
Har ila yau mataimakiyar shugaban ƙasar ta bukaci Amurkawa da magoya bayanta su amince da sakamakon zaben da aka kammala.
Abinda Harris da Trump suka tattauna a waya
"Zuciyata cike take da godiya bisa yardar da kuka nuna mani, cike take da ƙaunar ƙasarmu. Ya zama dole mu rungumi sakamakon zaɓe."
"Ɗazu na kira Shugaba Trump kuma na taya shi murnar nasarar da ya samu, na faɗa masa za mu taimaka masa wajen miƙa mulki cikin lumana."
- Kamala Harris.
Mataimakiyar shugaban Amurka dai ta amince da shan kaye a zaɓen Amurka, sannan ta tabbatar da cewa za ta taimaka domin a mika mulki cikin lumana.
Wannan dai na zuwa ne bayan Trump ya buga Harris da ƙasa, inda jam'iyyarsa ta Republican ta samu gagarumar nasara a zaben ranar Talata da ta gabata.
Elon Musk ya magantu kan nasarar Trump
A wani rahoton, an ji cewa Elon Musk ya yi magana kan nasarar Donald Trump a zaɓen shugaban ƙasan Amurka da aka gudanar a ranar Talata.
Attajirin ya bayyana cewa mutanen kasar Amurka sun ɗauki ragamar kawo canji sun miƙa ta a hannun Donald Trump.
Asali: Legit.ng