Awanni Kadan da Nasarar Trump, Attajiri Elon Musk Ya Samu Kazamar Riba, An Fadi Adadi
- Nasarar Donald Trump a Amurka ta jawowa attajirin duniya, Elon Musk riba inda dukiyarsa ta karu da $13bn cikin awanni kadan
- Musk wanda ya ke goyon bayan takarar Trump tun daga tushe ya samun ribar a hannayen jari da dama a kamfaninsa na Tesla
- Wannan na zuwa ne bayan sanar da nasarar Trump karo na biyu a zaben kasar Amurka inda ya kayar da Kamala Haris
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Amurka - Awanni kadan bayan lashe zaben Donald Trump a kasar Amurka, Elon Musk ya samu kazamar riba.
Mai kamfanin X, Musk ya samu ribar $13bn bayan abokinsa, Trump ya yi nasarar lashe zaben shugaban kasa.
Donald Trump Musk ya samu kazamar riba
CNN ta ruwaito cewa masu zuba hannun jari sun ce nasarar Donald Trump ta zama alheri ga kamfanin Musk na Tesla.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasarar ta kara daga darajar hannayen jari miliyan 411 da fiye da $13bn bayan gudunmawar $119m da ya ba kamfen din Trump.
Daily Trust ta ce babu wani attajiri ko dan kasuwa a duniya da ya goyi bayan Trump fiye da Musk a zaben da aka gudanar.
Gudunmawar da Elon Musk ya ba Trump
Bayan gudunmawar $119m ga Trump, attajirin ya sha fita yakin neman zabensa a lokuta da dama.
Har ila yau, Musk ya yi hira ta musamman da Trump a manhajarsa ta X kafin gudanar da zaben a Amurka.
Mafi yawan ƙaruwar arzikin Elon Musk ya faru ne saboda yawan gudunmawa da kamfanoninsa na Tesla da SpaceX ke samu daga gwamanti tsawon shekaru.
Elon Musk ya magantu bayan nasarar Trump
A baya, kun ji cewa Elon Musk ya yi magana kan nasarar Donald Trump a zaɓen shugaban ƙasan Amurka da aka yi a ranar Talata 5 ga watan Nuwambar 2024.
Attajirin ya bayyana cewa mutanen Amurka sun ɗauki ragamar kawo canji sun miƙa ta a hannun Donald Trump a karo na biyu a ƙasar.
Musk na ɗaya daga cikin attajiran duniya masu goyon bayan Donald Trump domin ya yi nasara kan abokiyar hamaƴyarsa Kamala Harris.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng