Trump Ya Yi Gaba a Zaben Amurka, Ya Fara Shinshino Nasara kan Kamala Haris
- Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi zarra a zaben da Amurka ta, ya yi nasara a manyan jihohi shida
- Wannan na nufin akwai babbar barazana na yiwuwar Kamala Haris ta zama shugabar Amurka mace ta farko a tarihin kasar
- Yanzu haka Trump ya yi nasara a jihohi kamar su Pennsylvania, Georgia, North Carolina, Wisconsin, Michigan da Arizona
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Amurka - Saura kiris dan takarar Republican kuma tsohon shugaban kasa Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka na 2024.
Trump dai ya samu nasara a mafi yawancin jihohin Amurka irinsu Nebraska da Georgia da Nevada North Carolina da Pennyslvania.
AP ta wallafa cewa tuni aka rufe rumfunan zabe, inda Trump ke a kan gaba, ita kuma Kamala Harris ta samu nasara a jihohi irinsu New York da New jersey da Oregon da Rhode Island.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Donald Trump na yin zarra a zaben Amurka
Tun da misalin 11:00 n.y Donald Trump ya fara samun nasara a jihohin Pennsylvania da 67% na kuri'a da aka kidaya, a Wisconsin ya samu 59%, a Michigan 27%; Georgia 90%; Arizona 50% North Carolina 86%.
Legit ta ruwaito cewa wadannan jihohi na da matukar muhimmanci a zaben Amurka kuma akwai yiwuwar za su taka rawa wajen tabbatar masa da nasarar zama shugaban kasa.
Trump na samun nasara a zaben Amurka
Sai dai tuni Trump ya kusa cika sharadin samun kuri'ar wakilan masu zabe 270 inda kawo yanzu ya samu kuri'u 266, kuri'a hudu kadai ta rage ya yi nasara.
Ana ganin yawan kuri'un da Trump ya samu na nufin ana dab da ayyana shi a matsayin zabebben shugaban kasar Amurka karo na biyu.
Zaben Amurka: Trump ya fara hango nasara
A baya kun ji cewa tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya yi gaba a zaben da Amurkawa ke gudanarwa inda za su zabi sabon shugaba a tsakaninsa da Kamala Haris, mataimakiyar shugaban kasa a yanzu.
Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa yanzu, Trump na jam'iyyar Republican ya samu kuri'un wakilan masu zabe 248 daga cikin 270 da ake bukata domin lashe zaben shugaban kasan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng