Trump v Kamala: Wanda Ke kan Gaba a Zaben Shugaban Kasan Amurka

Trump v Kamala: Wanda Ke kan Gaba a Zaben Shugaban Kasan Amurka

  • Donald Trump na jam'iyyar Republican ya fara jin ƙamshin sake komawa fadar White House a matsayin shugaban ƙasar Amurka
  • Tsohon shugaban ƙasan na kan gaba inda ya ba abokiyar hamayyarsa, Kamala Harris ta jam'iyyar Democrat, a ƙuri'un da aka kada
  • Trump ya samu ƙuri'un wakilan masu zaɓe 248 daga cikin 270 da ake buƙata domin lashe zaɓen shugaban ƙasan Amurka a 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Amurka - Donald Trump na kan gaba a zaɓen shugaban ƙasan Amurka, inda ya ba abokiyar hamayyarsa, Kamala Harris tazara.

Donald Trump ya samu ƙuri'un wakilan masu zaɓe 248 cikin 270 da ake buƙata domin samun nasara a zaɓen.

Trump na shirin lashe zabe
Donald Trump ya ba Kamala Harris tazara Hoto: Kamala Harris, Donald J. Trump
Asali: Facebook

Jaridar Associated Press ta rahoto cewa Trump yana kan gaba a jihohin da ba a riga an bayyana ba irin su Michigan da Wisconsin.

Kara karanta wannan

Fadan daba ya jawo sanadiyyar rasa rayukan mutane a Benue

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Donald Trump ya ba Kamala Harris tazara

A ranar Laraba, tsohon shugaban ƙasa, Trump ya lashe Pennylsvania, inda ya yi nasara a kan Kamala Harris a jihar mai matuƙar muhimmaci.

Dukkanin ƴan takarar biyu sun yi yaƙin neman zaɓe sosai a jihar, suka ziyarceta fiye da sauran jihohi.

Trump ya lashe ƙuri'un wakilan masu zaɓe 19 na Pennsylvania, shekara huɗu bayan ya sha kashi a hannun Joe Biden a jihar.

Tun daga shekarar 1948, babu ɗan takarar jam'iyyar Democrat da ya taɓa lashe zaɓen shugaban ƙasa ba tare da yin nasara a jihar Pennsylvania ba.

Ya zuwa yanzu Trump na jam'iyyar Republican ya samu ƙuri'un wakilan masu zaɓe 248 daga cikin 270 da ake buƙata domin lashe zaɓen shugaban ƙasan.

Malami ya yi magana kan zaɓen Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban cocin Inri Evangelical, Primate Elijah Ayodele, ya nemi 'yan Amurka da ma al'ummar duniya da su shirya abin da ke shirin faruwa a zaben ƙasar.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Najeriya ya ce ba zai ji haushin matarsa ba ko tana neman maza

Primate Elijah Ayodele ya yi iƙirarin cewa za a yi kare jini biri jini a zaben shugaban ƙasar Amurka na ranar Talata, 5 ga watan Oktoban 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng