Trump vs Harris: Malamin Addini Ya Hango Abin da ke Shirin Faruwa a Zaben Amurka

Trump vs Harris: Malamin Addini Ya Hango Abin da ke Shirin Faruwa a Zaben Amurka

  • Malamin addinin nan na Najeriya, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya ce za a yi kare jini biri jini a zaben shugaban kasar Amurka
  • A cikin wani sabon bidiyo, Primate Ayodele, ya yi hasashen makomar manyan 'yan takara a zaben; Donald Trump da Kamala Harris
  • Legit Hausa ta rahoto cewa Amurka na amfani da tsarin wakilan masu zaɓe (Electoral College) maimakon yawan kuri'un da aka kada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Shugaban cocin Inri Evangelical, Primate Elijah Ayodele, ya nemi 'yan Amurka da ma al'ummar duniya da su shirya abin da ke shirin faruwa a zaben kasar.

Primate Elijah Ayodele ya yi ikirarin cewa za a yi kare jini biri jini a zaben shugaban kasar Amurka da ake kan gudanarwa a yau Talata, 5 ga Oktoba.

Kara karanta wannan

'Akwai Kwankwaso': Omokri ya jero kusoshi a siyasar Najeriya da suka kayar da Atiku a 2023

Malamin addini ya yi magana kan sakamakon zaben shugaban kasar Amurka
Primate Ayodele, malamin addini, ya ce za a yi kare jini biri jini a zaben shugaban Amurka. Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Kamala Harris, Donald Trump
Asali: Facebook

Malami ya hango sakamakon zaben Amurka

A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, wanda Legit Hausa ta gani, malamin addinin ya ce zaben shugaban Amurka zai kasance 'zaben da bai kammalu ba.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakazalika, malamin ya yi ishara da cewa babu wani dan takarar da zai samu adadin kuri'un da ake bukata domin yin nasara a zaben.

A cewar Primate Elijah Ayodele:

“Gaskiya, zaben zai yi tsauri sosai. Abin da na gani shi ne cewa zaben zai kasance wanda bai kammalu ba. Babu wanda zai sami adadin kuri'un wakilan masu zabe."

Fafatawa tsakanin Trump da Harris a Amurka

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Donald Trump na yunkurin komawa fadar White House, abin da ba a saba gani ba.

A hannu daya kuma, mataimakiyar shugaban kasar, Kamala Harris ke neman kafa tarihi a matsayin mace ta farko kuma bakar fata da ta zama shugabar Amurka.

Kara karanta wannan

"Ban faɗi zaɓen 2023 ba," Atiku Ya Fallasa Yadda Tinubu Ya Masa Karfa-Ƙarfa

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta karshe da jaridar New York Times da kwalejin Siena suka yi ta gano cewa Trump da Harris sun yi kunnen doki a kuri'un da aka kada.

Kalli bidiyon malamin a kasa:

Yadda ake zaben shugaban kasar Amurka

Tun da fari, mun ruwaito cewa kasar Amurka na amfani da tsarin wakilan masu zabe (Electoral College) maimakon yawan kuri'un da al'umnma suka kada.

Yayin da ake ba kowace jiha adadin wakilan masu zabe, wannan tsarin na nufin cewa dan takarar da ya samu yawan kuri'un jama'a ba lallai ya ci zaben ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.