Hankula Sun Tashi bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Takarar Shugaban Kasa

Hankula Sun Tashi bayan 'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Takarar Shugaban Kasa

  • Ƴan bindiga sun hallaka ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙasar Mozambique na jam'iyyar adawa ta Podemos, Paulo Guambe
  • Ƴan bindigan sun kuma hallaka lauyan babban ɗan takarar jam'iyar adawa, Elvino Dias wanda suke tare da Paulo Guambe
  • Kisan mutanen biyu dai na zuwa ne yayin da ake jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasan wanda za a bayyana a ranar, 24 ga watan Oktoban 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙasar Mozambique - An harbe lauyan babban ɗan takarar jam'iyyar adawa a Mozambique, Venancio Mondlane, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen ranar 9 ga Oktoba a Maputo a ranar Asabar.

Ƴan bindiga sun kashe lauyan mai suna Elvino Dias, tare da wani ɗan takara, Paulo Guambe, na jam'iyyar Podemos da ke goyon bayan Venancio Mondlane.

Kara karanta wannan

Mutane kusan 100 sun rasu sakamakon fashewar tankar mai a Jigawa

An kashe dan takarar shugaban kasa a Mozambique
'Yan bindiga sun kashe dan takarar shugaban kasa a Mozambique Hoto: @zenaidamz
Asali: Twitter

Yadda ƴan bindiga suka kashe mutanen

Shaidu sun bayyana cewa wasu ƴan bindiga guda biyu sun harbi motarsu yayin da ta tsaya a kan hanyar da ke tsakiyar babban birnin ƙasar, cewar rahoton France24.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban jam'iyyar Podemos, Albino Forquilha ya tabbatar da kashe mutanen guda biyu, rahoton Bloomberg ya tabbatar.

Ƙungiyar lauyoyin ƙasar ta bayyana kisan da aka yi wa Elvino Dias a matsayin abin baƙin ciki.

Ƴan sanda sun ce an fara bincike amma ba su bayyana sunayen mutanen biyu da aka kashe ba.

Ana jiran sakamakon zaɓe a Mozambique

Kisan dai na zuwa ne yayin da ƙasar dakon sakamakon zaɓen shugaban ƙasan da aka gudanar wanda za a bayyana a ranar, 24 ga watan Oktoba a hukumance.

Venancio Mondlane, wanda ya ƙalubalanci jam'iyyar Frelimo da ke mulkin Mozambique tun bayan samun ƴancin kai shekara 49 da suka gabata, ya yi iƙirarin samun nasara a zaɓen.

Kara karanta wannan

Ana batun warware rikicin PDP, 'yan daba sun farmaki sakatariyar jam'iyyar

Ƴan bindiga sun harbi shugaban rundunar tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun harbi darakta janar na rundunar Askawaran Zamfara (CPG), Janar Lawal B. Muhammad (mai ritaya).

Ƴan bindigan sun harbi Janar Muhammad ne a lokacin da suka kai hari kan masu ababen hawa a ƙauyen Kucheri da ke ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng