Bankin Duniya Ya ba Gwamnatin Tinubu Shawara kan Maido Tallafin Man Fetur

Bankin Duniya Ya ba Gwamnatin Tinubu Shawara kan Maido Tallafin Man Fetur

  • Bankin Duniya ya ba gwamnatin Bola Tinubu shawara kan maganar maido tallafin man fetur da wasu tsare-tsare da ya kawo
  • Daraktan bakin duniya a Najeriya, Dr Ndiame Diop ya ce Tinubu ya rike tsare tsaren da ya kawo domin tabbatar da cigaban kasa
  • Ministan tattalin arziki, Wale Edun ya nuna amincewa da shawarin da aka ba gwamnatin kuma ya bayyana wani shirin da suke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bankin Duniya ya sake ba gwamnatin tarayya shawara kan riko da tsare tsaren Bola Tinubu.

Hakan na zuwa ne yayin da yan Najeriya ke cigaba da kira ga Bola Tinubu ya dawo da tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, gwamnatin Tinubu ta kawo karshen tallafin canjin kudi da na fetur

Tinubu
Bankin duniya ya shawarci Tinubu kan tsare tsaren gwamnati. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa ministan kudin Najeriya ya nuna amincewa da shawarar da aka ba gwamnatin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shawarar bankin duniya kan tallafin mai

Bankin duniya ya bukaci gwamnatin Najeriya ta kaucewa sauraron masu kira a dawo da tallafin man fetur da soke karya darajar Naira.

Daraktan bankin duniya a Najeriya, Ndiame Diop ne ya ba gwamnatin tarayya shawara a birnin tarayya Abuja yayin wani taro.

Ndiame Diop ya ce Bola Tinubu ya kara rike tsare tsaren da ya kawo da kyau domin farfaɗo da tattalin Najeriya. Ga abin da yake cewa:

Duk da cewa za a sha wahala a yanzu, amma riko da tsare tsaren ne kawai hanyar samar da cigaba a Najeriya.
Idan kuma aka kuskura aka canza tsare-tsaren, Najeriya za ta shiga cikin mummunan bala'i

- Ndiame Diop, daraktan bankin duniya a Najeriya

Kara karanta wannan

Gwamna a Arewa ya juyawa Tinubu baya, ya ce manufofinsa ne suka kawo yunwa

Minista ya karbi shawarae bankin duniya

Ministan kudi, Wale Edun ya nuna amincewa da shawarar da Ndiame Diop ya bayar.

Wale Edun ya ce idan aka canza shawara aka dawo da tallafin man fetur da dawo da darajar Naira an bata lokaci kan abin da aka yi a baya.

Pulse Nigeria ta wallafa cewa Edun ya ce a yanzu haka suna ƙoƙarin ganin sun kawo karshen tashin farashin kayayyaki a faɗin Najeriya.

Tinubu zai raba kuɗi ga talakawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar fara raba kuɗi ga talakawan Najeriya ta asusun banki.

Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana shirin, ya ce aƙalla talakawa miliyan 20 ne za su ci gajiyar tallafin nasu a fadin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng