Buhari Ya Tura Tsofaffin Ministocinsa 10 Yin Ta'azziya, Ya ba Iyalan Ministarsa Shawara

Buhari Ya Tura Tsofaffin Ministocinsa 10 Yin Ta'azziya, Ya ba Iyalan Ministarsa Shawara

  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kadu da babban rashi da tsohuwar Ministarsa ta yi a Najeriya
  • Muhammadu Buhari ya tura tawagar tsofaffin Ministocinsa guda 10 domin yi wa Pauline Tallen ta'azziyar rashin ɗanta
  • Wannan na zuwa ne bayan mutuwar dan Ministar guda daya tilo a duniya mai suna Richard Adamu Tallen a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi ta'azziya ga tsohuwar Ministarsa, Pauline Tallen a birnin Tarayya, Abuja.

Buhari ya tura tsofaffin Ministocinsa 10 domin yi mata ta'azziya bayan mutuwar ɗanta, Richard Adamu Tallen a karshen makon da ya gabata.

Buhari ya jajantawa tsohuwar Ministarsa kan rashin da ta yi
Muhammadu Buhari ya tura tsofaffin Ministocinsa 10 ta'azziya ga tsohuwar Ministarsa, Pauline Tallen. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Buhari ya yi ta'azziya ga Pauline Tallen

Kara karanta wannan

Badakalar N33bn: Yadda tsohon ministan Buhari ya siya kadarori da kudin kwangila

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Garba Shehu ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Ministan sadarwa, Lai Mohammed wanda ya jagoranci tawagar ya kadu da rashin da aka yi.

Lai ya ce tabbas an yi rashin matashi haziki wanda hakan abin takaici ne matuƙa ga iyalai da kuma yan uwa da abokan arziki.

"Ya riga mu gidan gaskiya wanda kuma hakan abin takaici ne da bakin ciki."

- Muhammadu Buhari

Buhari ya bukaci Tallen da iyalanta da su yi kokarin hakuri kan rashin da suka tafka na ɗansu.

Ministoci 10 da Buhari ya tura domin ta'azziya

Bayan Lai Mohammed da ya jagoranci tawagar akwai tsohon Ministan makamashi, Injiniya Abubakar Aliyu da na muhalli, Barista Mohammed Abdullahi.

Sauran sun hada da tsohon karamin Ministan makamashi, Jedy Agba da na harkokin Neja Delta, Umana Umana da na masana'antu, Niyi Adebayo.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Wike ya bayyana abin da zai kawo zaman lafiya

Sai kuma tsohon Ministan matasa, Sunday Dare da na kasashen waje, Geoffrey Onyeama da na sufuri, Muazu Jaji sai kuma albarkatun ruwa, Injiniya Sulaiman Adamu.

Tsohuwar Minista ta rasa ɗanta 1 tilo

A baya, mun ba ku labarin cewa tsohuwar Ministar harakokin mata a mulkin Muhammadu Buhari, Mrs Pauline Tallen ta yi rashi.

Tallen ta yi rashin ɗanta guda daya tilo a duniya mai suna Richard Adamu Tallen a karshen makon jiya a wani asibiti da ke birnin Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.