Fetur Zai Iya Kara Tsada, Rikicin Gabas ta Tsakiya Ya Jawo Tashin Farashin Danyen Mai

Fetur Zai Iya Kara Tsada, Rikicin Gabas ta Tsakiya Ya Jawo Tashin Farashin Danyen Mai

  • Farashin gangar danyen mai ya tashi a duniya bayan harin ramuwar gayya da Iran ta kai kasar Isra'ila
  • An ji shugaban Amurka, Joe Biden ya na cewa ana tattauna martanin Isara'ila da yiwuwar kai hari Iran
  • Duk da ba a samu matsala wajen cinikin danyen mai ba, amma tsoron abin da ka je ya zo ya jawo tashin farashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

America - Kalaman shugaban kasar Amurka, Joe Biden na yiwuwar kai hari kasar Iran da yakin da ke gudana a gabas ta tsakiya ya fara shafar mai.

Yanzu haka farashin gangar danyen mai ya tashi a kasuwar duniya, inda gangar danyen mai nau’in Brent ya kai $77, daidai da N130,000 a kudin Najeriya.

Kara karanta wannan

Iran vs Isra'ila: Gwamnati ta aika sakon gaggawa ga 'yan Najeriya mazauna Lebanon

Kasar
Farashin danyen fetur ya karu a kasuwar duniya Hoto: Twenty47studio
Asali: UGC

Jaridar Reuters ta wallafa cewa yan kasuwa sun shiga dar-dar kan yiwuwar Isra'ila ta kai hari kan matatun Iran, da kuma tsoron ita Iran din ta yi ramuwar gayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana fargabar karancin mai a kasuwar duniya

Kasar Iran na daga cikin kasashen da ke fitar da danyen mai a fadin duniya, kuma ta kan fitar da ganguna akalla miliyan 3.2 a kullum.

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa ana fargabar idan yaki ya balle tsakanin Iran da Isra'ila da taimakon Amurka, ba ya ga hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza da Lebanon, za a samu gagarumar matsala.

Iran na da muhimmanci a kasuwar mai

Iran ce kasa ta bakwai a masu fitar da danyen mai zuwa kasuwar duniya, inda ya fi alaka da kasar Sin, kamar yadda BBC ta wallafa.

Tun bayan harin da Iran ta kai kasar Isara'ila bayan kisan shugaban Hezbollah, Hassan Nasralla, farashin fetur a kasuwar duniya ya karu da 10%.

Kara karanta wannan

Najeriya @64: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu zai yi domin ceto kasa a halin kunci

Yan kasuwa za su sauke farashin fetur

A baya mun ruwaito cewa manyan yan kasuwar fetur a kasar nan sun bayyana cewa an samu saukin farashin sauke man fetur, wanda hakan na nufin za a samu saukin man.

A daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke tattaunawa da matatar Dangote, yan kasuwa sun ce an shigo da lita miliyan 141 na man fetur daga kasashen waje zuwa Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.