Rikici Ya Dauki Sabon Salo, Sojin Isra’ila Sun Kashe Shugaban Sojojin Hezbollah a Lebanon

Rikici Ya Dauki Sabon Salo, Sojin Isra’ila Sun Kashe Shugaban Sojojin Hezbollah a Lebanon

  • Yanzu muke samun rahoton yadda sojin Isra’ila suka kai farmaki kan dakarun Hezbollah a yankin Dahieh
  • An ruwaito cewa, ana fargabar sojin Isra’ila sun hallaka shugaban dakarun Hezbollah Hassan Nasrallah
  • Amurka ta bayyana matsayarta kan irin wadannan hare-hare da Isra’ila ke kai wa a yankin Larabawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Beirut, Lebanon - A wani sabon harin da sojin Isra’ila suka kai a ranar Juma’a a birnin Beirut, sun hallaka shugaban dakarun Hezbollah, Hassan Nasrallah.

Wannan na zuwa ne daga wata majiya da jami’in da ya shaidawa CBS, kamar yadda BBC ta tattaro.

Sai dai, wani rahoton ya bayyana cewa, shugabannin sojin Isra’ila sun ce batun ya yi wuri a bayyana ko Nasrallah ya kwanta dama.

An hallaka shugaban dakarun Hezbollah
Yadda Isra'ila ta kai hari Lebanon, ta hallaka shugaban Hezbollah | Hoto: SHUTTERSTOCK
Asali: UGC

Barnar da sojin Isra’ila suka yi

An tattaro cewa, harin na Isra’ila ya ruguza gine-gine da dama a Dahieh, wurin da dakarun Hezbollah ke fakewa a birnin.

Kara karanta wannan

An yi kuskure: Buba Galadima ya ambaci dan takarar shugaban kasa daya da ya fi Tinubu nagarta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar mai magana da yawun rundunar tsaron Isra’ila, Rr Adm Daniel Hagari, tabbas cikin kwarewa da daidaito sun kai farmaki kan hedkwatar mayakan Hezbollah, kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Ya zuwa yanzu, rahotanni sun ce, akalla mutum shida ne suka mutu a harin, yayin da sama da 91 ke kwance a asibiti, inji ma’aikatar lafiya ta kasar Lebanon.

Idan baku manta ba, shugaban Isra’ila, Netanyahu ya sha alwashin kawo karshen Hezbollah, inda harin ya zo jim kadan bayan maganar tasa a birnin New York.

Dalilin da yasa Isra’ika ke kai hari kan Hezbollah

A cewar shugaban na Isra’ila, dakarunsa za su ci gaba da kai hari kan Hezbollah a burinsu na dawo da akalla Isra’ilawa 70,000 da aka raba da gidajensu a Arewacin Isra’ila.

Sai dai, Amurka ta ce bata da ta cewa game da harin na Dahieh. A bangare guda, shugaba Joe Biden ya ba da umarnin bincike kan lamarin tare da duba hanyar habaka sojin Amurka a yankin na Labarawa.

Kara karanta wannan

Shirin zanga zanga a watan Oktoba ya girgiza gwamnatin Tinubu, an fara lallaɓa matasa

Ya kuma umarci dukkan ofisoshin jakadancin Amurka a yankin da su dauki matakan kariya da suka dace daidai gwargwado.

Taimakon da Iran ta nema kan yakin Isra'ila da Falasdinu

A wani labarin, shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya ce akwai bukatar kasashen Musulmi su fara daukar matakin kawo ƙarshen ta'addancin Isra'ila.

Shugaban Masoud Pezeshkian ya yi kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin Ministan harkokin kasashen waje na Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani.

Jaridar Xinhua net ta wallafa cewa shugaba Pezeshkian ya ce lokaci ya yi da dukan kasashen Musulmi da ke mutunta dokar kasa da kasa za su cure wuri guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.