Tinubu Na Kokarin Canza Ministoci, an Kitsawa Shugaban Kasa Juyin Mulki a Benin

Tinubu Na Kokarin Canza Ministoci, an Kitsawa Shugaban Kasa Juyin Mulki a Benin

  • Jami'an tsaro a kasar Benin sun sanar da cafke mutane uku kan zargin kitsa juyin mulki ga shugaban kasa Patrice Talon
  • An ruwaito cewa cikin mutane ukun da aka kama akwai kwamandan sojoji da wasu makusanta shugaban kasar biyu
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ya fara shirin sauya wasu daga cikin ministocinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Benin - Rahotanni da suka fito daga kasar Benin a Afrika ta Yamma sun nuna cewa an samu yunkurin juyin mulki.

An ruwaito cewa ana zargin wasu makusanta shugaban kasa Patrice Talon ne suka shirya kifar da gwamnatinsa.

Kasar Benin
An yi yunkurin juyin mulki a Benin. Hoto: Evaristosa
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa jami'an tsaron kasar sun yi nasarar cafke wasu daga cikin waɗanda ake zargin.

Kara karanta wannan

"Sai an sake zama:" Sanatan APC ya nemi Tinubu ya kira taron gaggawa kan tattali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama kwamanda kan juyin mulki a Benin

Jaridar the Cable ta wallafa cewa a ranar Laraba aka kama kwamandan sojoji kan zargin kifar da gwamnatin shugaba Patrice Talon a Benin.

Bincike ya nuna cewa kwamandan da aka kama shi ne yake jagorantar rundunar da ke ba shugaban kasar tsaro.

An kama ministan kasar Benin kan juyin mulki

Bayan kwamandan sojojin, an kuma kama tsohon ministan wasannin kasar, Oswald Homeky wanda ake zargi yana da hannu cikin kitsa juyin mulkin.

Dadin dadawa, an kama wani shahararren dan kasuwa mai suna Olivier Boko wanda babban abokin shugaban kasar ne a cikin wadanda ake zargi.

Yaushe aka shirya yin juyin mulki a Benin?

Bayanai sun nuna cewa waɗanda ake zargin sun shirya aiwatar da juyin mulkin ne a ranar Jumu'a, 27 ga watan Satumba.

A halin yanzu, lauyoyin tsohon ministan wasannin sun bukaci a gaggauta sake shi inda suka ce kama shi ya saba doka.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga tsaka mai wuya kan korar Ministoci, an taso shi a gaba

APC ta yi zargin juyin mulki a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta shirya domin fara zanga zangar nuna goyon baya ga shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Rahotanni sun nuna cewa sakataren kungiyar shugabannin APC na jihohi, Alphonsus Ogar Eba ne ya bayyana haka a Abuja kan zargin juyin mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng