Albishir ga Yan Baiwa: Tsohon Shugaban Amurka, Trump Ya Ƙirƙiro Manhajar Kirifto
- Tsohon shugaban kasar Amurka wanda yake neman shugabanci a karo na biyu ya fito da sabuwar manhajar kudin Kirifto
- Donald Trump ya kirkiro sabuwar manhajar Kirifto ne tare da hadin gwiwar ƴaƴansa da wasu abokan hulɗarsa na kasuwanci
- A baya, shugaba Donald Trump ya kasance mai kin jinin hada hada da kudin Kirifto kafin ya sauya tunaninsa a wannan karon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Tsohon shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kirkiro sabuwar manhajar kudin Kirifto a duniya.
Dan Donald Trump ya bayyana cewa sabuwar manhajar za ta kawo sauyi sosai a harkar kudin Kirifto a duniya da tattalin arziki.
Jaridar the Economic Times ta wallafa cewa Donald Trump ya yi haɗaka ne da yayansa da kuma abokansa na kasuwanci wajen samar da manhajar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manhajar Kirifto da Trump ya kirkiro
Tsohon shugaban kasa kuma dan takara a Amurka, Donald Trump ya kirkiro manhajar Kirifto mai suna World Liberty Financial.
Punch ta wallafa cewa iyalan Donald Trump sun bayyana samar da manhajar ne a yammacin ranar Litinin kuma ana sauraron karin bayani daga garesu.
A baya, Donald Trump ya kasance mai adawa da harkar Kirifto amma a wannan karon ya nuna goyon baya dari bisa dari kan amfani da kuɗin Kirifto a duniya.
Yadda Kirifton Trump zai yi aiki
Daga cikin hada hadar da za a yi da Kirifton World Liberty Financial akwai ba mutane damar rance da tara kudin Kirifto.
Haka zalika an ruwaito cewa manhajar za ta kawo tsarin da zai takaita shigowar bankuna cikin hada hadar kudin Kirifto.
Wasu jiga jigai wajen samar da manhajar, Zachary Folkman da Chase Herro sun ce a karon farko manhajar za ta yi amfani ne da stablecoins wanda suke da alaka da Dalar Amurka.
An kai wa Donald Trump hari
A wani rahoton, kun ji cewa an kai wa dan takarar shugaban kasar Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump hari a yayin da ya ke wasan golf ranar Lahadi.
Wannan dai shi ne karo na biyu da Trump ke tsallake rijiya da baya, a wancan karon sai da barbashin harsashi ya same shi a kunne.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng