Zaben Amurka: An Sake Kai wa Donald Trump Hari, An Bayyana Halin da Ya Ke Ciki

Zaben Amurka: An Sake Kai wa Donald Trump Hari, An Bayyana Halin da Ya Ke Ciki

  • An kai wa dan takarar shugaban kasar Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump hari a yayin da ya ke wasan golf ranar Lahadi
  • Wannan dai shi ne karo na biyu da Trump ke tsallake rijiya da baya, a wancan karon sai da barbashin harsashi ya same shi a kunne
  • A martanin da tsohon shugaban Amurkan ya yi, ya ce yana nan cikin koshin lafiya kuma hare-haren ba za su hana shi fafutuka ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Amurka - Dan takarar shugaban kasar Amurka na jam'iyyar Republican, Donald Trump ya tsallake rijiya da baya a ranar Lahadi.

An rahoto cewa hukumar leken asirin Amurka ta yi nasarar dakile abin da hukumar FBI ta kira da wani yunkuri na kashe Trump.

Kara karanta wannan

"Da mu muke mulki, ba za a janye tallafin fetur kamar yadda Tinubu ya yi ba," inji shugaban PDP

An sake kaiwa Donald Trump hari, ya ce ya na cikin koshin lafiya
Trump ya tsallake rijiya da baya yayin da jami'an tsaro suka harbi wani dan bindiga. Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

An farmaki Donald Trump a Amurka

An bayyana cewa an kaiwa Donald Trump hari ne yayin da yake wasan golf a wani filinsa da ke West Palm Beach, Florida, inji rahoton Reuters.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an leken asiri sun hango kuma sun harbe wani dan bindiga a cikin daji kusa da filin wasan, kimanin tazarar yadi dari daga inda Trump ya ke tsaye.

An cafke wanda ya nemi harbe Trump

Hukumomi sun ce wanda ake zargin ya jefar da bindiga kirar AK-47 da wasu kayayyaki a wurin inda ya gudu a mota amma daga baya aka kama shi.

Ba a bayyana ko ta yaya wanda ake zargin ya san Trump na filin wasan golf a lokacin ba, amma yunkurin harin ya jawo ayar tambaya game da kariyar da ake ba shi.

"Ina cikin koshin lafiya" - Trump

Kara karanta wannan

Dan takarar shugaban kasa na neman muƙamin mataimaki a 2027? ya yi magana

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya tabbatar wa magoya bayansa cewa “yana cikin koshin lafiya” bayan yunkurin harin da aka kai masa.

Kafar labaran Aljzeera ta rahoto Trump ya yi magana ne kan lamarin a wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na tara kudi yana mai cewa:

“Ka da ku ji tsoro! Ina cikin koshin lafiya, kuma babu wanda ya ji rauni. Na godewa Ubangiji.”
"Amma, akwai mutane a cikin wannan duniyar da za su iya yin komai domin dakatar da mu. Ba zan daina fafutuka a kanku ba. Ba zan taba mika wuya ba."

- Donald Trump

Donald Trump ya samu rauni

Tun da fari, mun ruwaito cewa dan takarar shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sha dakyar bayan an harbe shi yayin da ya ke jawabi a taro a Pennsylvania.

An ga Donald Trump a wani bidiyo ya na yamutsa fuska kuma ya yi saurin dafe kunnensa kafin ya duka yayin da harsashin bindiga ya kuskuresa a taron.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.