IMF Ya Fadawa Tinubu Gaskiyar Halin da Talaka ke Ciki, Ya Buƙaci a Saukaka Lamura

IMF Ya Fadawa Tinubu Gaskiyar Halin da Talaka ke Ciki, Ya Buƙaci a Saukaka Lamura

  • Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya bayyanawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu halin kuncin rayuwa da ake a Najeriya
  • IMF ya tabbatar da cewa akwai buƙatar samar da hanyoyin da za su kawo sauki ga talakawa saboda halin da suke ciki a kasar nan
  • Haka zalika IMF ya yi magana kan dogayen layuka da ake samu a Najeriya saboda ƙaranci da wahalar man fetur kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Asusun ba da lamuni na duniya ya yi kira na musamman ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan tsadar rayuwa.

IMF ya ce ya zama dole a samar da hanyoyin da za su kawo sauki ga talaka bayan cire tallafin man fetur da aka yi a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamna Zulum ya yi bayanin halin da ake ciki, ya faɗi kuɗin da Tinubu ya turo

Bola Tinubu
IMF ya yi magana ga Tinubu kan tsadar rayuwa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wakilin IMF a Najeriya, Dakta Christian Ebeke ne ya isar da sakon ga gwamnatin tarayya.

IMF ta ce ana wahala a Najeriya

Wakilin IMF, Dakta Christian Ebeke ya ce magana ta gaskiya ana shan wahala a Najeriya a karkashin mulkin Bola Ahmed Tinubu.

Dakta Christian Ebeke ya ce wahalar da ake sha ta samu asali ne daga tsare tsaren da gwamnatin Bola Tinubu ta kawo a Najeriya.

IMF: Wahalhalun da ake sha a Najeriya

Asusun ba da lamuni ya ce a yanzu haka ana fama da masifar tsadar abinci a fadin Najeriya da sauran kayayyaki.

IMF ya ce bayan matsalolin abinci da ake fuskanta sai ga shi an kara tunkarar matsalar ambaliyar ruwa a kasar.

IMF ya bukaci a saukakawa talakawa

IMF ya bayyana cewa akwai tsananin buƙata gwamnatin Bola Tinubu ta fitar da hanyoyin da za ta rage raɗaɗi ga talakawan Najeriya.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Rundunar sojoji ta mika ta'azziyya Borno, za a taimaka wa jama'a

Dakta Christian Ebeke ya ce ya kamata a fitar da shirin tallafi da zai rage raɗaɗin cire tallafin mai da sauran matsalolin da ake fuskanta.

An bukaci Tinubu ya cire tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar yan kasuwar man fetur sun kara fuskantar Bola Ahmed Tinubu kan wasu bukatu na musamman.

Cikin abubuwan da yan kasuwar suka bukata akwai neman gwamnatin tarayya ta cire hannu a kan tallafin man fetur gaba daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng