Babu Najeriya: Jerin Kasashe 10 na Duniya da Suka Fi Tsadar Fetur a 2024
Najeriya na ci gaba da fama da wahalar karancin man fetur da kuma tsadarsa. Sai dai kuma kasar ba ta a cikin jerin kasashen duniya mafi tsadar man.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Duk da cewa farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi zuwa kimanin N1000 a wasu jihohin Najeriya, hakan bai sa kasar ta zama mai arhar fetur a duniya ba.
Shafin kididdiga na Globalpetrolprices ya fitar da jadawalin kasashen da suka fi sayar da fetur da tsada da kuma masu sayar da shi da arha.
Farashin man fetur a kasashen duniya
A cikin jadawalin, wanda The Cable ta tattara ya nuna cewa Najeriya ba ta a cikin kasashe 10 na duniya masu tsadar fetur, amma tana biye a bayansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An rahoto cewa an buga bayanan farashin fetur a kasashen ne ta hanyar amfani da canjin dalar Amurka zuwa Najeriya a kan N1587.142/$1, a ranar 26 ga Agustan 2024.
Amma idan aka yi la'akari da cewa a yanzu ana canjin dala da Naira a kan 1590.42/$1, za mu iya cewa akwai yiwuwar farashin fetur a kasashen duniya ya kara tashi.
Kasashen duniya masu tsadar fetur
Duba jerin kasashen duniya masu tsada da kuma arhar fetur a kasa:
SN | Sunayen kasashe | Farashin fetur |
1 | Birtaniya | N2,973 |
2 | Kamaru | N2,270 |
3 | Kanada | N2,101 |
4 | Afrika ta Kudu | N2,035 |
5 | Sin | N1,939 |
6 | Togo | N1,851 |
7 | Jamhuriyar Benin | N1,797 |
8 | Ghana | N1,582 |
9 | Amurka | N1,532 |
10 | Daular Larabawa/UAE | N1,267 |
11 | Najeriya | N770 |
12 | Aljeriya | N544 |
13 | Angola | N525 |
14 | Libiya | N51 |
15 | Iran | N46 |
Dangote ya fitar da samfurin fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa murna ta karade a Najeriya yayin da matatar man Dangote ta sanar da cewa ta fara fitar da samfurin man fetur din da ta tace.
Ranar Talata, 3 ga watan Satumbar 2024 shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Aliko Ɗangote, ya nunawa duniya sumfurin man matatar.
Wannan babbar nasara ce ga matatar man Dangote wadda ta fuskanci kalubale mai tarin yawa tun daga lokacin da ta fara gudanar da ayyukanta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng