Gwamnati Ta Yanke Matsaya kan Turawa da aka Zarga da Daga Tutar Kasar Rasha

Gwamnati Ta Yanke Matsaya kan Turawa da aka Zarga da Daga Tutar Kasar Rasha

  • A bisa dukkan alamu gwamnatin Nijeriya ta yanke matsaya kan yan ƙasar Poland da ta kama bisa zargin daga tutar Rasha
  • Jami'an tsaro sun zargi mutanen da hannu wajen shirya zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya da aka yi a farkon wata
  • Sai dai ministan harkokin wajen Poland, Radoslow Sikorski ya bayyana cewa a yanzu haka an sake mutanen kasar tasu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An samu bayanai kan wasu dalibai yan kasar Poland da aka kama a Najeriya a lokacin zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Ministan harkokin wajen kasar Poland, Radoslow Sikorski ne ya bayyana halin da ake ciki game da mutanen.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta sha alwashin ceto dukkanin mutanen da ke hannun miyagu

Tutar Rasha
An sake turawa da aka kama kan daga tutar Rasha. Hoto: Mudassir Ibrahim Mando Kaduna
Asali: Facebook

Legit ta tatttaro bayanai kan halin da ake ciki ne a wani bidiyo da ministan harkokin wajen Poland, Radoslow Sikorski ya wallafa a shafisa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin Turawa kan daga tutar Rasha

Gwamnatin Najeriya ta kama yan kasar Poland a jihar Kano yayin da yan Najeriya ke zanga zangar adawa da tsadar rayuwa.

Haka zalika jami'an tsaro sun zargi mutanen da jawo daga tutar Rasha da kuma hannu a cikin zanga zangar.

An saki Turawan Poland a Najeriya

BBC Hausa ta wallafa cewa a halin yanzu gwamnatin Najeriya ta sake dalibai da malaminsu da aka kama a lokacin zanga zanga.

Bincike ya nuna cewa mutanen tawaga ce ta dalibai da malaminsu da suka zo Najeriya daga jami'ar Warsaw.

'Yan kasar Poland sun koma Kano

Ministan harkokin wajen Poland ya tabbatar da cewa a yanzu haka mutanen sun koma Kano domin cigaba da harkokinsu.

Kara karanta wannan

Salon yaki ya canza: Gwamna ya ba da izinin luguden wuta ga yan bindiga

Radoslow Sikorski ya kara da cewa nan gaba kadan za su koma ƙasar Poland idan suka gama abin da ya kawo su.

Rasha ta yi magana kan daga tutarta

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Rasha ta musanta raɗe-raɗin tana da hannu a ɗaga tutocin da matasa masu zanga-zanga suka yi a Najeriya.

Ofishin jakadancin Rasha a Najeriya ya ce gwamnatin Shugaba Putin ba ta sa baki a harkokin cikin gida na kowace ƙasa a duniya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng