Pavel Durov: Waye Shugaban Manhajar Telegram da Dalilan Cafke Shi a Faransa?
Jami'an tsaro a Paris, kasar Faransa sun cafke Pavel Durov, shugaban kamfanin Telegram da a yanzu ke kan ganiya saboda amfaninta wajen harkar 'mining.'
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Paris, France - Jami'an tsaro sun kama ɗaya daga shugabannin kamfanin Telegram, Pavel Durov lokacin da ya isa filin jirgin Paris-Le Bourget daga Baku a kasar Azerbaijan.
Jami'an tsaron kasar Faransa sun kama Durov bisa zarginsa da wasarere da abubuwan da ke wakana a manhajarsa ta Telegram.
Legit ta zakulo yadda Mista Durov ya samar da manhajar mai mabiya sama da Biliyan 1 tare da danuwansa, da zarge-zargen da ake masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waye Shugaban Manhajar Telegram?
Aljazeera ta wallafa cewa Pavel Durov, ɗan shekaru 39 ne da ya shahara wajen kirkirar manhajojin zamani.
A shekarar 2007, ya samar da wata manhaja ta Vkonte a mahaifarsa ta St Petersburg, wanda aka kwatanta tasirinta da Facebook.
Bayan ya sha matsin lamba daga gwamnatin Rasha ne ya sayar da kasonsa a manhajar a shekarar 2014.
Yaushe aka samar da manhajar Telegram
Daga shekarar 2014 ne Mista Durov ya mayar da hankali wajen tayar da.manhajar Telegram da ya samar da haɗin gwiwar ɗan uwansa, Nikolai.
Ya samar da manhajar ya na da shekaru 28, wanda yanzu ta yi shura wajen matasa masu harkar 'mining,' amma hukumomi na ganin akwai matsala.
Zarge-zargen da ake yiwa mai Telegram
CNBS ta tattaro cewa an kama Mista Pavel Durov ne bisa zargin ana aikata ɓarna a manhajarsa ta Telegram, amma ko a jikinsa.
Daga cikin abubuwan da ake zargin ana aikatawa ta manhajar akwai zamba, safarar kwaya, rura wutar ta'addanci da sauran laifuka, batun da kamfanin ya musanta.
An cafke shugaban kamfanin Telegram
A baya mun ruwaito cewa jami'an tsaro sun cafke shahararren matashin attajiri mai kamfanin Telegram, Pavel Durov bayan ya sauka a filin jirgi da ke Faransa.
Hukumomi na zargin Mista Durov da yin sakaci ana amfani da manhajarsa wajen miyagun ayyuka da su ka hada da safarar kwayar, ta'addanci da zamba.
Asali: Legit.ng