Ana Shirin Zanga Zanta Ta 2, an Gano Halin da ake ciki bayan Kifar da Gwamnatin Bangladesh

Ana Shirin Zanga Zanta Ta 2, an Gano Halin da ake ciki bayan Kifar da Gwamnatin Bangladesh

  • Rahotanni na nuni da cewa da yawa daga cikin dalibai da suka yi zanga zanga a kasar Bangladesh sun shiga mummunan hali
  • Wasu daga cikin dalibai sun bayyana halin da suke ciki bayan yan sanda sun harbe su da harsashi sun jawo musu makancewa
  • Jami'an lafiya a asibitoci sun yi bayani kan halin da ake ciki wajen yin jinyar marasa lafiya da aka raunata lokacin zanga zangar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Bangladesh - Dalibai da suka shiga zanga zangar da ta jawo kifar da gwamnatin Bangladesh sun yi bayanin halin da suke ciki.

Wani dalibi mai suna Umar Faruq ya bayyana cewa an jawo ya rasa ganinsa inda yake jinya a asibiti.

Kara karanta wannan

Bacin ciki: Jihohin Najeriya 6 da mutane 43 suka rasa rayukansu daga cin abinci

zanga zanga
Dalibi ya makance yayin zanga zanga. Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

Jaridar Yahoo News ta wallafa cewa ma'aikatan lafiya sun ce masu jinya sun musu yawa bayan kammala zanga zangar da kifar da gwamnatin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da Umar Faruq ke ciki

Wani dalibi mai shekaru 20, Umar Faruq ya bayyana cewa yan sanda sun harbe shi da harsashin roba a fuska kuma hakan ya jawo masa makancewa.

Umar Faruk wanda a yanzu haka yana babban asibitin Bangladesh ya ce har yanzu yana da fatan cewa kasar za ta dawo turba mai kyau.

Sauran mutanen da aka jikkata

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an kashe mutane akalla 450 a lokacin zanga zangar wanda ake zargin yawanci yan sanda ne suka kashe su.

Haka zalika an samu mutane da dama da aka raunata wasu an makantar da su yayin da aka harbe su.

Halin da ake ciki a asibitin Bangladesh

Kara karanta wannan

Matasa sun kwaci yan fashi a hannun yan sanda, sun cinnawa 1 wuta

Mukaddashin Daraktan asibitin NIOH, Dakta Mohammed Abdulqadir ya ce ba su taba samun tarin marasa lafiya kamar na wannan lokacin ba.

Dakta Mohammed Abdulqadir ya ce saboda yawan marasa lafiya suna iya yin tiyata 10 a lokaci daya.

Sojoji sun karbi mulki a Bangladesh

A wani rahoton, kun ji cewa mulkin firaministar Bangladesh, Sheikha Hasina na shekaru 15 ya zo karshe bayan ta yi rubuta takardar murabus.

Murabus din Sheikha Hasina na zuwa ne bayan shefe watanni ana zanga-zangar adawa da matakin gwamnatinta na rusa guraben ayyuka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng