Zanga Zanga: Abin da Kasar Poland Ta ce kan Kama Mutanenta 7 da DSS Ta yi a Kano

Zanga Zanga: Abin da Kasar Poland Ta ce kan Kama Mutanenta 7 da DSS Ta yi a Kano

  • Rahotanni sun ce jami’an tsaron Najeriya sun tsare wasu ‘yan kasar Poland da suka hada da dalibai shida da malami daya
  • An alakanta Turawan guda 7 da daga tutocin kasar Rasha yayin zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki a Najeriya
  • Ma'aikatar harkokin wajen Poland ta ce mutanenta da ake tsare da su ba su shiga zanga-zangar ba, suna daukar hotuna ne kawai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kasar Poland ta musanta cewa ‘yan kasarta da jami’an tsaro suka kama a jihar Kano sun daga tutar kasar Rasha a lokacin da ake zanga-zangar yunwa a Najeriya.

Poland ta ce 'yan kasarta sun leka inda ake yin zanga-zangar ne domin su kashe kwarkwatar idanunsu tare da daukar hoto ba wai don su shiga ciki ko daga turar wata kasa ba.

Kara karanta wannan

Yunwa na barazana ga rayukan almajiran Kano, an roki matasa su hakura da zanga zanga

Kasar Poland ta yiwa jami'an tsaron Najeriya martani kan kama 'yan kasarta 7
Zanga Zanga: Poland ta ce 'yan kasarta ba su daga tutar Rasha a Kano ba. Hoto:Khalipha Umar
Asali: Facebook

Poland ta yiwa DSS martani

A cewar wani rahoto da jaridar The Punch ta fitar, ma'aikatar harkokin kasar wajen Poland ce ta yiwa jami'an tsaron Najeriya wannan martanin a ranar Lahadi, 11 ga Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa jami'an DSS sun tabbatar da kama 'yan kasar Poland din 7 da zargin cewa sun shiga zanga-zanga tare da daga tutocin kasar Rasha a jihar Kano.

Ma’aikatar harkokin wajen ta ce

"Daliba shida da malaminsu daya 'yan kasarmu ba su shiga zanga-zangar, suna daukar hotuna ne kawai lokacin da aka kama su."

Kamfanin labaran TVP World da ke a kasar ta Poland ya ruwaito cewa, daliban 6 da malaminsu sun je halartar wani taro ne a jami’ar Bayero ta Kano.

Jami'ar Warsaw ta yi magana kan dalibanta

An ce 'yan kasar ta Poland sun kasance daliban nazarin Afirka a kwalejin nazarin gabas ta tsakiya a jami'ar Warsaw.

Kara karanta wannan

Sunayen jihohi da bayanan 'yan siyasan da ake tuhuma kan daga tutocin Rasha

Jami’ar yada labarai ta jami’ar Warsaw, Anna Modzelewska, ta ce sakin daliban shi ne babban abin da makarantar ta sa gaba.

Modzelewska ta ce:

“Yantar da daliban UW (jami'ar Warsaw) shine fifikonmu. Dole ne mu yi duk abin da za mu iya domin hakan ta tabbata cikin sauri."

Poland ta roki a saki 'yan kasarta

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin kasar Poland ta bakin mataimakin ministan harkokin wajen kasar Jakub Wisniewski, ta roki Najeriya da ta saki mutanenta da aka kama.

A kan idan sun daga tutar Rasha, mataimakin ministan ya ce, "Ba zan iya yarda da wannan ikirarin ba. Muna kira ga Najeriya da ta saki mutanemu su koma ga iyalansu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.